An Nemi Bindige Jirgin da Ya Yi Yunkurin Ceto Wadanda Yaki Ya Rutsa da su a Sudan

An Nemi Bindige Jirgin da Ya Yi Yunkurin Ceto Wadanda Yaki Ya Rutsa da su a Sudan

  • Mayakan da ke yaki a Sudan sun kai wa wani jirgin saman C-130 hari yayin da ya zo ceto Turkawa
  • Rundunar sojin kasar Sudan tana zargin ’yan sa-kai na RSF da harbin jirgin kasar wajen a Khartoum
  • Rundar RFF ta karyata zargin da ake yi mata, ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi ta na nan

Sudan - Rahotanni sun tabbatar da cewa an harbi wani jirgin saman C-130 da ya nemi ya dauke mutanen Turkiyya da yaki ya rutsa da su a kasar Sudan.

Rahoton da aka samu daga Reuters ya ce a sakamakon harbin da aka yi ne ya yi saukar gaggawa a filin tashi da saukar jirage na Wadi Seyidna a Khartoum.

Ma’aikatar tsaro ta kasar Turkiyya ta tabbatar da wannan lamari a karshen makon nan, amma ta ce babu ko mutum guda da ya yi rauni a sanadiyyar harin.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Mahaukaci Yake Tafiyan Kilomita Da Yawa Zuwa UNIBEN a Kullun, Ya Zauna Yana Rubutu

Gwamnatin Turkiyya ba ta zargi kowa a kan abin da ya faru ba, illa iyaka ta ce an yi amfani da kananan makamai wajen kai wa jirgin saman na ta hari.

Jawabin ma’aikatar tsaron Turkiyya

"An harbi jirginmu na C-130 da ya je kubutar da mutane da kananan makamai, amma jirgin ya sauka lafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da ba a samu wani rauni a kan ma’aikatanmu ba, za a gudanar da binciken da suka dace a kan jirgin."

- Ma'aikatar tsaron Turkiyya

Jirgin sama
Wani jirgin C-130-Hercules Hoto: www.theaviationzone.com
Asali: UGC

"Babu ruwanmu" - RFF

Sojojin Sudan sun ce mayakan kasar ne suka harbo jirgin saman, suka bata masa gidan mai.

Rahoton da BBC ta fitar ya nuna dakarun RSF sun karyata zargin nan, sun bayyana cewa sun tsagaita wuta na awanni 72 kamar yadda aka yi yarjejeniya.

A wasu hotuna da aka samu daga shafin Mahmod Gamal a Twitter, an ga yanayin barnar da aka yi wa jirgin, har ta kai ana zargin gidan mai ya fara yoyo.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Zanga-Zanga Ya Barke A Yayin Da Jami'an Najeriya Da Ke Aikin Kwaso Mutane 'Suka Tsere Daga Sudan'

Lambar jirgin ya tabbatar da yana da rajista ne da jiragen saman zirga-zirgar sojojin Turkiya- C130, a ranar Juma’a ya yi saukar ungulu a fili da ke Khartoum.

Rayuwa sun salwanta a yaki

The Guardian ta ce ana maganar an kashe mutane akalla 512 a sanadiyyar yakin da ya barke.

Baya ga haka, mutane kusan 4, 200 ne majalisar dinkin Duniya ta tabbatar da sun samu rauni, mutanen da suka tsere daga Sudan kuwa sun haura 20, 000.

Za a ceto 'Yan Najeriya

A baya an ji labarin irin yunkurin da ake yi na tattaro mutanen kasar Najeriya kusan 2400 da mummunan yakin da ake yi a Sudan ya rutsa da su a halin yanzu.

Ministocin harkokin kasar waje sun ce gwamnati ta ware $1.2m domin dawo da 'yan kasarta. Kafin Saudi Arabiya ta dauke wasu ‘Yan Najeriya ta jiragen ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng