An Bar ‘Yan Najeriya Cirko-Cirko, Sudan ta Hana Mutanen Afrika Ficewa a Tsakiyar Yaki

An Bar ‘Yan Najeriya Cirko-Cirko, Sudan ta Hana Mutanen Afrika Ficewa a Tsakiyar Yaki

  • Gwamnatin tarayya tana cigaba da yin bakin kokarinta na ceto daliban Najeriya da ke kasar Sudan
  • A dalilin yakin da ake yi, an samu matsala wajen shiga da ’Yan Najeriyar cikin iyakar Ethiopia
  • Idan an yi nasara, a ranar Talata mutum fiye da 2000 za su kubuta daga Sudan, su dawo kasarsu

Abuja - A ranar Litinin 24 ga watan Afrilu 2023, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa daliban Najeriya sun makale a Sudan a Arewacin Afrika.

Punch ta ce an hana wadannan Bayin Allah da ake kokarin kubutarwa daga kasar Sudan shiga kasar Ethiopia mai makwabtaka da kasar Larabawan.

Gwamnatin Najeriya ta ce jami’anta na bakin kokarin shawo kan wannan lamari yayin da ake fama da yaki tsakanin bangarorin sojojin kasar ta Sudan.

Hukumomin kasar nan sun ce jami’an gwamnati da ke Ethiopia su na neman yadda za a fice da daliban Najeriya da aka dauko daga makarantun Sudan.

Kara karanta wannan

Yakin Sudan: Peter Obi Ya Yi Tuni 1 Mai Muhimmanci Ga Shugaba Buhari

Ana cikin dar-dar a Sudan

Jaridar ta ce gwamnatin tarayya ta nuna yana da da hadari dalibai suyi kokarin dawowa Najeriya a yanzu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana haka ne sai aka ji Sakataren gwamnatin Amurka, Antony Blinken yana bada sanarwar cewa Hafsoshin sojojin na Sudan sun amince a tsagaita wuta.

Sudan
Dakarun Sojojin Sudan Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sai dai za a dakatar da yakin ne na tsawon sa’o’i 72 wanda hakan zai ba kasashen ketare damar sulalewa da mutanensu da rikicin ya rutsa da su a Sudan.

Amurka ta tsoma baki

Antony Blinken ya nuna gwamnatin Amurka ta na shirin hada-kai da abokan huldarta domin kafa kwamiti da zai kawo karshen yakin da ya barke.

Daga daren yau dai ake sa ran yaki ya tsaya tsakanin RFF da SAF, har zuwa nan da kwanaki uku. The Nation ta ce mutum 2800 ake sa ran dawowarsu yau.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Kashe Mayaka 35, Sun Lalata Sansanonin Boko Haram a Wata Jahar Arewa

Jami’an hukumar NEMA masu bada agajin gaggawa sun ce gwamnatin Najeriya ta nemi tayi amfani da majalisar dinkin Duniya wajen ceto ‘yan kasarta.

Hakan bai yiwu ba domin majalisar dinkin Duniyan ba ta amince da rokon ba a sakamakon hallaka ma’aikatanta biyar, dole za a bi ta kan hanyar mota.

Taron kasashe a Ghana

Rahoto ya tabbatar da Muhammadu Buhari zai halarci taron kolin Shugabannin kasashen yankin tekun Guinea a garin Accra, babban birnin kasar Ghana.

Femi Adesina ya ce Shugaban Kasa Buhari zai gabatar da jawabi a taron wanda zai tattauna a kan dabarun zaman lafiya da kuma magance manyan laifuffuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng