Mutane Da Dama Masu Azumin Jiran Haɗuwa Da Yesu Sun Kwanta Dama
- Ƴan sanda a ƙasar Kenya sun gano gawarwakin wasu mutum huɗu da suka mutu a cikin daji
- Mutanen sun mutu ne yayin da suke azumi a cikin daji domin jiran haɗuwa da Yesu Almasihu
- Tuni jami'an ƴan sanda suka cafke faston da ya ba su wannan fatawar da yin wannan azumin
Kenya - An samu gano wasu gawarwakin mutum 4 ranar Alhamis a ƙasar Kenya bayan sun ɗauki azumin jiran haɗuwa da Yesu Almasihu.
Wasu mutane da dama su ma da suka ɗauki azumin an garzaya da su zuwa wani asibiti dake a yankin Kilifi domin duba lafiyar su, cewar rahoton BBC Hausa.
Jami'an ƴan sanda sun tabbatar cewa wata fatawa da wani fasto ya bayar itace dalilin da ya sanya mutanen suka ɗunguma zuwa daji domin gudanar da bautar.
Africanews ta ce hukumomi sun ƙara da cewa sun samu nasarar ceton mutum 11, waɗanda 6 daga cikinsu sun ƙanjame duk suna cikin halin ƙaƙanikayi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ƴan sanda sun sanar da cewa za su ci gaba da binciken sauran mutanen a yau Juma'a, saboda rahotanni sun tabbatar mutanen masu azumin haɗuwa da Yesu na da yawa a cikin dajin.
Ƴan sanda sun tabbatar cewa sun gano wani sabon kabari a cikin dajin amma za su yi bincike a kansa a ranar yau Juma'a.
Mutanen masu gudanar da aikin bautar, mabiya wata coci ne da ake kira da suna Good News International wacce wani fasto ke gudanar da ayyukanta.
Ƴan sanda sun kama faston
A yanzu haka yana ƴan sanda sun cafke faston akan zargin tuhumar sa da ba mutanen cocin sa umurnin zama da yunwa, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga ciki da niyyar haɗuwa da Yesu.
Jami'an ƴan sandan sun kuma tabbatar da cewa ba za su iya bayar da belin faston ba, domin ko a watan da ya wuce sai da aka tuhume shi kan mutuwar wasu yara 2 waɗanda iyayensu na cikin mutanen da ke yin azumin.
Fasto Ya Kwaikwayi Azumin Annabi Isa Na Kwana 40, Ya Mutu a Kwana Na 25
A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda wani fasto ya sheƙa barzahu yayin da ya ke kwaikwayon azumin Annabi Isah na kwana 40.
Faston ya kasa jurewa inda ya ce ga garin ku nan lokacin da ya kai kwana na 25 yana azumin.
Asali: Legit.ng