An Yi Sabon Attajirin Duniya, An Samu ‘Dan Shekara 74 da Sha Gaban Elon Musk

An Yi Sabon Attajirin Duniya, An Samu ‘Dan Shekara 74 da Sha Gaban Elon Musk

  • Idan aka tambaye ka wanene ya fi kowa kudi a Duniya, daga yau to ka da ka ce Elon Musk ne
  • Duk Duniya yanzu babu mai kudin da yake gaba da Attajirin kasar Faransar nan, Bernard Arnault
  • A yau Arnault ya ba Dala biliyan 200 baya, dukiyarsa ta nunka ta Bill Gates sau biyu har da kari

America - A yanzu maganar da ake yi, Elon Musk ya tashi daga zama Attajirin Duniya, an samu wani mai kudin da ya zarce shugaban kamfanin Twitter.

Ba kowa ne ya sha gaban Elon Musk ba illa Bafaranshen nan, Bernard Arnault mai shekara 74. Mujallar Forbes ta tabbatar da wannan lamari a makon nan.

Mai kudin Faransar wanda shi ne shugaban kamfanin LVMH ya mallaki Dala biliyan 211.

Kara karanta wannan

Rayyuka 17 Sun Salwanta A Sabon Rikici Da Ya Barke A Jihar Arewa

Kamfaninsa LVMH ne yake da su Louis Vuitton, Christian Dior, Givenchy, Tiffany’s, Marc Jacobs, Sephora da suka samu riba mai tsoka a ‘yan watannin baya.

An maimaita abin da ya faru a 2022

Mujallar ta ce ba wannan ne karon farko da Musk ya rasa wurinsa ga Mista Bernard Arnault ba, hakan ya faru da shugaban kamfanin SpaceX a karshen 2022.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baya ga SpaceX masu kera motocin Tesla, Inc, Musk ya mallaki kamfanoni irinsu Neuralink da OpenAI, shi ne na biyu a Attajiran Duniya da Dala biliyan 180.

Attajirin Duniya
Bernard Arnault da Elon Musk Hoto: www.intelregion.com
Asali: UGC

BQ Prime ta ce a jerin masu kudin da ake da su yanzu, Larry Ellison ya yunkuro sama, yayin da shahararren mai kudin nan, Mista Bill Gates ya koma na shida.

Jerin manyan masu kudi da dukiyarsu:

1. Bernard Arnault da danginsa

Kara karanta wannan

An Karrama Jonathan a Kasar Waje Kan Abin da Ya Yi a Najeriya Shekaru 8 da Suka Wuce

Kudi: $211bn | Silar arziki: LVMH | Shekaru: 74 | Kasa: Faransa

2. Elon Musk

Kudi: $180bn | Silar arziki: Tesla, SpaceX | Shekaru: 51 | Kasa: Amurka

3. Jeff Bezos

Kudi: $114bn | Silar arziki: Amazon | Shekaru: 59 | Kasa: Amurka

4. Larry Ellison

Kudi: $107bn | Silar arziki: Oracle | Shekaru: 78 | Kasa: Amurka

5. Warren Buffett

Kudi: $106bn | Silar arziki: Berkshire Hathaway | Shekaru: 92 | Kasa: Amurka

6. Bill Gates

Kudi: $104bn | Silar arziki: Microsoft | Shekaru: 67 | Kasa: Amurka

7. Michael Bloomberg

Kudi: $94.5bn | Silar arziki: Bloomberg LP | Shekaru: 81 | Kasa: Amurka

8. Carlos Slim Helú da danginsa

Kudi: $93bn | Silar arziki: Kamfanonin sadarwa | Shekaru: 83 | Kasa: Mexico

9. Mukesh Ambani

Kudi: $83.4bn | Silar arziki: Abubuwa da yawa | Shekaru: 65 | Kasa: Indiya

10. Steve Ballmer

Kudi: $80.7bn| Silar arziki: Abubuwa da-dama| Shekaru: 65 | Kasa: Amurka

An karye a Najeriya

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun harbe shugaban APC a wata jiha, sun hallaka mazauna kauye

Wani rahoto da mu ka fitar ya nuna maku yadda kasuwanci miliyoyin Bayin Allah ya karye da Gwamnati ta canza kudi, ta kawo tsarin takaita yawonsu.

Kungiyar ASBON ta ce mutanen da suka rasa hanyar cin abinci ba su da kwarewa wajen sanin fasahar zamani, kamfanoni miliyan 25 suka karye a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng