Shugaba Zelensky na Ukraine zai gana da shugaba Xi na China nan ba da jimawa ba

Shugaba Zelensky na Ukraine zai gana da shugaba Xi na China nan ba da jimawa ba

  • Shugaban kasar Ukraine, mai girma Zelensky ya ce kasarsa ta shirya karbar bakuncin shugaban kasar China Xi Jinping
  • Amurka na bayyana guna-guni kan yunkurin China na sulhunta tsakanin Rasha da Ukraine da ke yaki tun bara
  • Ya zuwa yanzu, kasashen biyu sun yi asarar sojoji da fararen hula tun farkon yakin a watan Faburairun bara

Kyiv, Ukraine - Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskiy ya gayyaci shugaban kasar China, Xi Jinping domin ziyartar kasar da ke Gabashin Turai.

Wannan na fitowa ne daga bakin Zelensky a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a wani taro mai muhimmanci, rahoton CNN.

A cewarsa, kasarsa ta shirya daram domin tarbar shugaban na China, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Zelensky ya gayyaci Xi kasarsa
Shugaba Zelensky na Rasha da Xi na China | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Mun shirya karbar shugaba Xi, inji Zelensky

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Ya Lissafa Kasashen Da Zai Iya Yin Hijira Saboda Bola Tinubu Ya Zama Zababben Shugaban Kasa

A kalaman Zelensky:

“Mun shirya don ganawa dashi a nan.”

Shugaba Xi na China dai bai taba magana da shugaban Ukraine ba tun bayan da kasar Rasha ta Putin ta kai mummunan farmaki kan mazauna Ukraine a watan Faburairun bara.

Sai dai, a watan da ya gabata ne China ta fitar da wasu manufofi 12 na yadda za a warware matsalolin da ke tsakanin Rasha da Ukraine, UkrinForm ta tattaro.

Xi ya tattauna kan batun rikicin da abokinsa na kut-da-kut, wato shugaban Rasha Vladimir Putin a lokacin da ya ziyarci birnin Moscow ta Rasha a makon jiya.

Sai dai, tattaunawar shugabannin biyu bata bayyana hanya kai tsaye na yadda za a kawo karshen yakin kasashen na Rasha da Ukraine ba.

Kadan daga abin da China ta yi kira akai shine, duba yiwuwar tsakaita wuta a yakin da aka kai kan kasar ta Ukraine.

Amurka na guna-guni kan yunkurin China na sulhunta Rasha da Ukraine

Kara karanta wannan

2023: An Kai Karar Hadimin Tinubu a Babban Kotun Duniya Saboda Bakaken Kalamai

Sai dai, duk da haka kasar Amurka na ci gaba da guna-guni kan yunkurin na China, inda tace shugaba Xi bai taba yin Allah wadai da abin da Rasha ta yiwa Ukraine ba.

A cewar Amurka, janyewar sojojin Rasha da kuma tsakaita wutar zai ba Putin damar ci gaba da nuna iko ga kasashen da ya mamaye da kuma sake hada sojoji masu karfi a nan gaba.

A bangarenta, Ukraine dai ta yi na’am da shiga tsakani na diflomasiyya da China za ta yi, amma Zelensky ya ce za a janye yankin ne kawai bayan sojojin Rasha sun tattara sun fice daga lardin Ukraine.

A baya, Zelensky ya bayyana kukan cewa, kasar Rasha na kokarin rusa masa kasa tare da hallaka al’ummar da yake mulka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.