Mutumin Da Ya Tsere Ya Bar Matarsa Da Da Tsawon Shekaru 33 Ya Dawo, Ya Nemi Wani Kason Gidansu
- Liu Yusheng ya tashi daga China zuwa Amurka shekaru 30 da su ka wuce, ya bar matarsa da yarinya yar shekara takwas
- Lokacin da ya ka sa samun aiki, ya dawo Shangai, da nufin dawowa wajen matarsa da yarsa bayan shekara 30
- Ya tarar gidan da ya bar su ciki hukuma ta rushe kuma an biya su da wani
- Liu ya bukaci matar da bari ya zauna a banagaren gidan da ke Shanghai ko ta biya shi rabin kudin hayar gidan ko ya dauki matakin shari'a in taki amincewa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani mutum da ya bar iyalinsa don neman kyakkyawar makoma ya dawo, ya na so a ba shi rabin kadararsu.
Dan kasar China Liu Yusheng ya bar matarsa da yarsa yayin da ya gudu kasar Amurka ba bisa ka'ida na shekaru 30 da suka wuce.
"Har Yanzu Ban Yi Kwanciyar Aure Ba Da Matata Shekara Uku Bayan Aure": Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Ta Ki Bari Su Raya Sunnah
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An sace fasfo, da kudin dan China a Amurka
Mutumin mai shekaru 73 wanda ya gudu Amurka tare da dan uwansa, da nufin samun ingantacciyar rayuwa, bai saka jin halin da iyalinsa ke ciki ba, kamar yadda South China Morning Post ta ruwaito.
Ya yi ikirarin cewa an sace ma sa fasfo da kudinsa, bai kuma samu aiki ba tsahon shekarun, sannan a titi ya ke kwana.
Da Liu ya dawo Shangai a watan Nuwambar 2022, bai iya gano inda matarsa da yarsa su ke ba.
Kungiyar yan Shanghai a Amurka
Kungiyar yan Shanghai mazauna Amurka su taimaka ma sa ya dawo dawo gida tare da taimaka ma sa ya samo adireshin matarsa da yarsa, amma iyalan na sa sun ki magana da shi.
Liu ya tuna cewa lokacin da ya tafi Amurka, hukumar kasar da ya ke aiki da ita ta ba shi gida wanda ya ke zaune da iyalansa.
Hukumomi sun rushe gidansa na Shanghai
Sai dai, an rushe gidan bayan shekaru, kuma hukuma ta biya iyalan da gidan da ya fi wancan girma.
Liu ya bukaci matarsa da ta bari ya zauna a rabin gidan a Shanghai ko ta biya shi rabin kudin gidan.
Yanzu haka, da ya ke zaune a matsugunin gwamnati a Shanghai, Liu ya yi barazanar daukar matakin shari'a idan matarsa taki amincewa da bukatunsa.
Matarsa ba ta mayar da martani a bayyane kan barazanar mijinta, wanda ya gudu ya bar ta da yarinya mai shekaru takwas.
"Na gaji da Dubai": Budurwa yar Najeriya ta zubar da hawaye a bidiyo
A wani rahoton daban kun ji cewa wata budurwa yar Najeriya wacce ke aiki a birnin Dubai da ke Hadadiyar Daular Larabawa, UAE, ta sharbi kuka a bidiyo tana mai cewa ta gaji da aiki a kasar.
Sai dai ta kuma koka cewa ba ta san yadda za ta sanar da mahaifiyarta a gida Najeriya cewa ta gaji tana son dawowa gida ba.
“Ta Tsere”: Matar Aure Ta Yashe Gaba Daya Asusun Bankin Da Suke Tara Kudi Da Mijinta, Ta Yi Batan Dabo
Asali: Legit.ng