Ma'aikaciya ta Tsinci N6.908 Miliyan Tana Hanyar Dawowa Daga Aiki, Ta Mayarwa Mai Kudin
- Wata mata 'yar kasar Michigan ta shiga kanun labarai saboda gaskiya da rikon amanarta bayan tsintar makudan kudi a jaka, wanda ta mayar wa masu shi duk da tana cikin matsin rayuwa
- An ruwaito yadda matar mai gaskiya ta tsinci kudi N6.908 miliyan cikin wata jaka a wani gidan gas a kasa, yayin da ta ke kan hanyarta na dawowa daga wurin aiki a kasa mai nisan 2.7 mil a kasa kamar kullum
- Sai dai, an gano wasu sabbin ma'aurata ne suka yar da kudin da aka basu gudunmawa ranar aurensu, lamarin da yasa aka bude mata gidauniyar tallafi wanda a yanzu an hada ma ta sama da $45,000 don ta mallaki mota
Wata mata 'yar birnin Michigan ta shiga kanun labarai saboda halin gaskiya da rikon amanarta wacce ta tabbatar ta mayar wa da sabbin ma'aurata kudinsu da ya bace.
Diane Gordon wacce take tattakin kusan mil uku zuwa aiki kullum tsawon shekara daya ta tsinci wata jaka dauke da $15,000 yayin da ta ke kan hanyar zuwa wurin aiki, kamar yadda FOX 2 Detroit ta ruwaito.
Ta mayarwa sabbin ma'auratan jakar kudin da ta tsinta a wajen gidan gas a tantagaryar kasa.
Gordon ta bayyana yadda ta ke madugun 2.7 mil zuwa aiki a kasuwar VC Fresh kullum bayan motarta ta lalace a watan Fabrairu, 2022.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda matar mai gaskiya ta bayyana, yayin da ta ke kan hanyarta na dawowa gida ranar 21 ga watan Janairu, inda ta tsaya a wani gidan gas yayin da ta lura da wata jaka da sununuwar dukiya makil da ita.
"Yayin da na kalli tantagaryar kasa na yi ido biyu da wata jaka da makudan kudade a ciki. Lokacin da na bude ta kudin da na gani yafi wanda nayi zato."
Ta ruwaito yadda ta yi tsuntuwar ga 'yan sanda, inda ta ce:
"Wannan ba mallakina bane."
Lt. Matthew Ivory na sashin ofishin 'yan sanda na White Lake ya ce a binciken da suka yi game da inda kudin ya fito jim kadan, sun gano yadda kudin ya zama mallakin wasu sabbin ma'aurata.
Ya kara da cewa:
"Babu wani abu da yazo ranta in ba ta kare wa kudin kallo ba. A cikin jakar akwai wasu katikan biki, wadannan kyautuka ne ga ma'auratan a wannan ranar da suka yi aure. Ina tunanin kudin sun kai $14,780."
Jami'in 'dan sandan ya bayyana yadda bayan maida kudin lami lafiya ga masu shi, wani a sashin ya shirya wata gidauniyar tallafi don tabbatar da Gordon ta mallaki sabuwar mota.
Jami'in ya ce:
"Dianne bata da mota, tana madugu ne zuwa da dawowa VC a kowacce rana, ba tare da dubi da nisan hanyar inda ta ke aiki kullum ba. Ita kanta tana bukatar kudi kuma hakan zai canza ma ta rayuwa, amma duba da bata yi tunanin kin maido da kudin ba abun yabawa ne."
Kamar yadda wanda ya bude gidauniyar tallafin ya bayyana, wanda a yanzu yafi $25,000 da ake bukaci a tara ma ta da kudi sama da $45,000.
The Times News ta rahoto cewa, abun da aka gani a jakar sabbin ma'auratan shi ne $14,780 wanda aka basu gudunmawa ranar aurensu.
"Dianne ta zama abar misali na dattako da rashin son kai duk da irin matsin rayuwar da ta ke ciki. Zamu yi da aiki da Scott Automotive don samar wa Dianne mota da kudin da aka tara."
- Suka ce.
Attajiri mai taimkon talakawa ya haukace, bidiyonsa yana kwasar rawa a kasuwa
A wani labari na daban, bidiyon wani mahaukaci yana kwasar rawa babu kida a kasuwa ya bayyana.
Wani ma'abocin amfani da Twitter ya gane shi inda yace a baya attajiri ne da ya kware a taimakon al'umma mabukata.
Asali: Legit.ng