Tashin Hankali Yayin Da Aka Tsinci Gawar Farfesan Najeriya Da Mace A Cikin Gida A Amurka
- Jami'an tsaro sun gano gawar Marinus Iwuchukwu, wani farfesa dan Najeriya mazaunin Amurka a gidansa
- Yan sandan sun kuma gano gawar wata mata mai suna Charce Dunn a cikin gidan tare da rauni a jikinsu
- Jami'ar Katolika na Duquesne, inda Iwuchukwu ya yi aiki har zuwa rasuwarsa ta yi ta'aziyya ga yan uwa da abokansa
Amurka - An tsinci gawar wani farfesa dan Najeriya mazaunin Amurka, Marinus Iwuchukwu da wata mata mai suna Charce Dunn a Pittsburg Pennsylvania, rahoton Vanguard'
An tsinci gawarsu ne a kan hanyar Thorncrest Drive, Wilkins Township Pittsburg a ranar Talata bayan korafin 'hayaniyar gida' misalin karfe 10 na safe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yan sanda na Allegheny sun ce sun samu kira na cewa su duba lafiyar farfesan da matan a gidansu.
A cewar yan sanda, wani mutum daban ya gaza tuntubar mutumin ya kuma gano an daba masa wuka. Wata mace na cikin gidan da bindiga.
Yan sanda na tawagar SWAT sun shiga gidan sun gano gawar wani mutum dan shekara 59 da wata mata yar shekara 50, Pittsburgh Action News ta rahoto.
Bisa alamu dukkansu biyu suna da rauni a jikinsu, ita kuma matar akwai alamar kaman ita ce ta yi wa kanta rauni da bindiga, in ji yan sandan.
Yan sandan sun ce ana cigaba da zurfafa bincike kan lamarin da ake zargin an yi kisa.
Jami'ar da Farfesan ke aiki ta mika sakon ta'aziyya ga iyalansa
A martanin ta kan lamarin, Jami'ar Katolika na Duquesne, inda Iwuchukwu ya yi aiki a matsayin mataimakin farfesa na nazarin addini kafin rasuwarsa, ta yi ta'aziyya ga iyalai da abokan marigayin malamin jami'ar.
Mai magana da yawun jami'ar, Gabriel Welsch, cikin wata sanarwa ya ce:
"Wannan abin bakin ciki ne gare mu baki daya kuma muna mika ta'aziyyar mu ga iyalan Farfesa Iwuchukwu, dalibansa, abokansa, da masoyansa."
Wani a Abuja ya kashe abokinsa ya birne gawarsa saboda rikici kan kudi
Yan sanda sun kama wani mutum dan shekara 63 mazaunin FCT, Abuja, Taiwo Ojo, kan zarginsa da halaka abokinsa mai suna Philip Kura.
Rahotanni sun bayyana cewa Ojo ya buga wa Philip shebur ne a kansa yayin da suke jayayya kan wani kudi sannan ya janye gawarsa ya boye a cikin wani dan karamin daji, daga bisani ya birne.
Asali: Legit.ng