Tsohon Mai Shekaru 97 Wanda Bai Taba Aure ba, Yayi Wuff da Zukekiyar Budurwa Mai Shekaru 30
- Wani tsohon saurayi mai shekaru 97, Johanna Arap Butuk, daga karshe ya fita sahun tuzurai bayan karar da gaba daya rayuwarsa a gaurontaka
- Tsohon da ya ga jiya ya ga yau ya ce ya zabi karasa rayuwarsa da masoyiyarsa Alice Jepkorir, wacce ke da shekaru 30 kamar yadda wani dan uwansa da ya bayyana
- Ma'auratan sun yi bikin kece raini cike da farin ciki mara misaltuwa, yayin da biyun suka yi alkawarin karasa rayuwarsu har abada a Soy, Uasin Gushu
Wani kaka mai shekaru 97 daga kasar Uasin Gishu, wanda bai taba auren wata mace ba a tsawon rayuwarsa ya shige daga ciki.
Tsohon saurayin daga birnin Soy a kasar Uasin Gishu ya auri masoyiyarsa ranar 14 ga watan Janairun 2023.
Bikin aurin kece rainin da tsohon tuzurun mai shekaru casa'in da wani abu yayi yana hararo 100 ya guduna ne ranar 14 ga watan Janairu, 2023, a Soy, cikin kasar Uasin Gishu inda fastoci daga majami'ar Katolika suka halarci taron bikin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yayin zantawa da TUKO.co.ke, Sally Chepkoech, wata 'yar uwar angon ta bayyana yadda tuzurun mai shekaru 97 bai taba aure ba a rayuwarsa, inda daga karshe yake farin cikin haduwa da dayan rabin jikinsa da tsufarsa.
"Wannan babban taron shagalin bikin ne, wanda fastoci daga majami'ar Katolika, wadanda suka zo harabar gidanmu don shagalin bikin suka halarta."
- Sally cikin farin ciki ta shaidawa manema labarai.
Sally ta ce, daga karshe tsohon ya amince da yin aure bayan ganin aurarrakin 'ya'yan 'yan uwa da dama.
"Shi din bai taba aure ba, saboda haka, bayan mun yi aure sai ya tambayi waye zai kula da shi, domin duk mun yi aure, sai dai da muka yanke shawarar nema masa matar da za ta kula da shi,"
- A cewarta.
Sally, wacce ta bayyana yadda Johanna yake yaya ga mahaifinta ta ce, matar mai shekaru 30 mai suna Alice ita ma tayi farin cikin samun wanda zai kula mata da 'ya'yanta hudu.
"Bikin ya matukar kayatarwa. Mun sha rawa tare da shi tare da kawayen amarya."
- A cewarta, inda ta kara da cewa bikin ya karfafa mutane da dama da kada su cire rai da soyayya.
Ta kara da bayyana yadda dangi suka cika da murnar yadda ya samu mata bayan kwashe shekaru aru-aru yana gwauro.
Katuwar damisa ta ratsa wurin shakatawa, tana takun kasaita kusa da mutane
A wani labari na daban, wata katuwar damisa ta bayyana a bidiyo inda aka ga ta ratsa cikin jama'a tana takuna kasaita.
Sai dai cike da abun mamaki, jama'ar ba su ko nuna tsoro ko damuwarsu ba kan yadda ta shigo cikinsu.
Asali: Legit.ng