Argentina Na Tunanin Saka Hoton Messi A Takardar Kudi, Hotuna Sun Bazu A Soshiyal Midiya
- Babban bankin kasar Argentina na duba yiwuwar saka fuskar Lionel Messi a takardar kudi na Peso 1,000, a cewar rahotanni
- Hakan na zuwa ne bayan gaggarumar nasarar da tawagar kwallon kafa na Argentina ta yi a gasar kofin duniya da aka yi a Qatar
- Tuni dai hotunan takardar kudin na Argentina da ake fatan za a fitar da hoton fuskar Messi da sauran yan tawagar na Argentina a baya ya bazu a intanet
Argentina - Bayan da fitaccen dan wasan ya jagoranci tawagar Argentina zuwa cin gasar kofin duniyarsu ta farrko tun bayan shekaru 36 a Mexico, ana ta tattauna batun sanya hotonsa a sabon takardar kudi ta Peso 1,000, Daily Mail ta rahoto.
A cewar wata jaridar kasar mai suna El Financiero, Babban Bankin Argentina ta kosa ta dauki matakin tunawa da nasarar da kungiyar kwallon kafa ta kasar ta samu a Qatar inda ta doke Faransa da ci 4-2.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tun wannan lokacin, kwafin takardar kudi na peso 1,000 da ake tattauna a kansu ya bazu a intanet da shafukan sada zumunta, yayin da maso sun kosa su ga an saki takardar kudin.
Yayin da an saka fuskar Messi a gefen kudin, lakabin 'La Scaloneta' na tawagar shi ake son a saka a bayan takardar kudin, rahoton Times Now.
An rika alakanta tawagar da sunan tun bayan da Lionel Scaloni ya gaji Jorge Sampaili a shekarar 2018.
Karkashin Scaloni, Argentina ta yi nasarar lashe kofin Copa America a 2021, da Finalissima a filin wasa na Wembley da kuma Kofin Duniya ta FIFA 2022.
Idan jami'an bankin ba su yi watsi da shirinsu na sakin takardar kudin ba - wanda ake imanin zai samu karbuwa wurin yan Argentina - zai zama karo na farko da ake saka tawagar kasar a takardar kudi.
An taba fitar da sulalla don nasarar cin kofin duniya da tunawa da first lady a Argentina
A baya sun taba fitar da sulalla a lokacin da Argentina ta lashe kofin duniyar ta na farko a 1978.
An kuma taba buga sulalla a yayin bikin shekaru 50 da tunawa da rasuwar Eva Peron, tsohon First Lady ta Argentina.
Ga hotunan a kasa:
Wani ya yi hasashen nasarar Messi a gasar kofin duniya
A wani rahoto, mutane suna ta jinjina wa wani mutum da aka ce ya yi hasashen nasarar Lionel Messi a gasar kofin duniya da aka yi a Qatar a 2022.
Jose Miguel Polanco, a wallafar da ya yi a Twitter a ranar 20 ga watan Maris na 2105 ya ce Lionel Messi zai yi nasarar zama zakaran kwallon kafa na duniya da ba a taba ganin irinsa ba a gasar.
Kotu Ta Yanke Wa Matashi Ɗan Shekara 20 Ɗaurin Gidan Yari A Jihar Arewa Saboda Lalata Allunan Kamfen Ɗin Atiku
Asali: Legit.ng