Kasar Saudiyya Ta Bai Wa Mahajjatan Najeriya Kujeru 95,000 a Hajjin 2023

Kasar Saudiyya Ta Bai Wa Mahajjatan Najeriya Kujeru 95,000 a Hajjin 2023

  • Yayin da ake sauraran Hajjin badi, kasar Saudiyya ta bayyana cewa, ta ba Najeriya adadin kujeru 95,000 a 2023
  • Kasar Saudiyya ta dawo wa da Najeriya wasu kudaden da aka samu matsala a kansu na mahajjan bana
  • A bara, kasar Saudiyya ta rage adadin mahajjata daga Najeriya saboda barkewar annobar Korona da ta addabi duniya

Abuja- Yayin da ake shirin shiga sabuwar shekarar 2023, kasar Saudiyya ta ba Najeriya adadin kujeru 95,000 na wadanda za su yi Hajjin badi.

Wannan adadi dai shine adadin da Saudiyya ta ba Najeriya a baya kafin barkwar annobar Korona a 2020.

Wannan batu na fitowa ne daga hukumomin kasar Saudiyya a cikin wata sanarwa a ranar Laraba 21 ga watan Disamban 2022.

Hakazalika, mai magana da yawun hukumar alhazai ta Najeriya, Suwaiba Ahmad ta tabbatarwa BBC Hausa wannan mataki na kasar ta Saudiyya.

Kara karanta wannan

Aiki ja: Hotunan yadda kyakkyawar budurwa ta sauya bayan shiga aikin soja sun girgiza intanet

Saudiyya ta ba Najeriya kujerun Hajji 95,000 a badi
Kasar Saudiyya Ta Bai Wa Mahajjatan Najeriya Kujeru 95,000 a Hajjin 2023 | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarta:

"Saudiya ta dawo wa da Najeriya kujerun da ta saba ba ta 95, 000, wanda a baya ta rage suka koma, 45, 000 saboda matsalar annobar korona, wanda shi din ma ba mu iya cikewa ba, saboda an bayar da shi a kurarren lokaci.”

Saudiyya ta dage wasu dokokin aikin Hajji

A bangare guda, kasar Saudiyya ta sanar da janye wasu ka’idojin da ta gindaya na takaita shekarun mahajjata, wanda aka fara kakabawa ‘yan kasashen waje a shekarar da ta gabata.

A nata bangaren, hukumar NAHCON mai kula da jigilar mahajjata ta ranar Talata ta ce, kasar Saudiyya ta dawo wa da Najeriya wasu kudaden da suka kai Riyal 542,033 (N107,864,567).

An dawo da kudaden abinci ga mahajjatan Najeriya

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, kudaden da Saudiyya ta dawo dasu na abincin da aka samu matsala ne da kamfanin Mutawwaifs mai kula da abincin mahajjata ‘yan nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

Labari mai kayatarwa: Ahmad Musa ya gina katafariyar cibiyar wasanni a wata jihar Arewa

Wannan dawo da kudi na zuwa ne bayan da wasu mahajjatan Najeriya suka yi korafi kan rashin samun wadataccen abinci a lokacin aikin Hajjin bana.

NAHCON ta ce, da zarar kudin shigo hannu, za ta mika su ga hukumomin jin dadin alhazai na jihohi don rabawa wadanda lamarin ya shafa.

A hajjin shekarar 2022 da ya gabata, kasar Saudiyya ta ba Najeriya kujeru 60,000 ne kacal, saboda annobar Korona, an rage adadin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.