Taliban Ta Sanar Da Haramtawa Mata Zuwa Jami'o'i A Afghanistan
- Gwamnatin Afganistan karkashin Taliban ta bada umurin dakatar da mata zuwa jami'o'i ba tare da bata lokaci ba
- Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ma'aikatar ilimin kasar ta aike wa jami'o'i masu zaman kansu da na gwamnati
- Akawai yiwuwar wannan takunkumin da Taliban ta saka kan ilimin mata zai iya janyo suka daga kasashen duniya
Aghanistan - Taliban ta sanar da rufe jami'o'i ga mata a Afghanistan a cewar wata wasika da ta fito daga ministan ilimin manyan makarantu.
Sanarwar ta ce za a cigaba da kasancewa a wannan yanayi har sai zuwa wani lokaci a nan gaba. Ana sa ran dokar zai fara aiki nan take, rahoton Daily Trust.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnatin Aghanistan na Taliban ta ce ba za a kyale mata su rika zuwa jami'o'in kasar ba har sai zuwa wani lokaci a gaba.
A cewar Aljazeera, wasikar, wacce kakakin ma'aikatar manyan makarantu na kasar ya tabbatar a ranar Talata, ta umurci jami'o'in gwamnati da masu zaman kansu su dakatar da dalibai mata nan take, bisa umurnin gwamnati.
Wasikar da aka raba wa dukkan jami'o'i masu zaman kansu da na gwamnati mai dauke da sa hannun Ministan Ilimin Manyan Makaratu, Neda Mohammed Nadeem ta ce:
"Ana sanar da ku da ku gaggauta aiwatar da umarnin da aka ambata na dakatar da karatun mata har sai an sanar da ku"
Hana mata zuwa jami'a na iya janyo wa Taliban suka daga kasashen duniya
Wannan takunkumin na baya-baya da Taliban ta saka kan ilimin mata na iya janyo suka daga kasashen duniya.
Mai magana da yawun ma'aikatan, Ziaullah Hashimi, wanda ya tabbatar da wasikar a Twitter, ya tabbatarwa kafafen watsa labarai da dama umurnin ciki har da AFP da Associated Press.
"Yana asassa tashin hankali": Taliban za ta hana amfani da TikTok a Afghanistan
A bangare guda, Taliban ta bayyana cewa tana shirin haramta amfani da manhajjar sada zumunta na TikTok saboda yana janyo karuwar ababen tada hankula.
A wata sanarwa da ta fito daga ma'aikatar sadarwa na kasar, ta ce za kuma ta haramta wani wasan bidiyo na intanet mai suna PUBG cikin yan makonni.
Taliban ta sanar da wannan sabon matakin ne bayan hana wasannin kwaikwayo na talabijin tare da lalata kayan kida da wakoki da sauran fina-finai.
Asali: Legit.ng