Elon Musk Ya Rasa Matsayinsa Na Attajirin Duniya, Kudinsa Ya Ragu Da N1.6tn Cikin Awanni
- Elon Musk ya rasa matsayinsa a matsayin mai kudin duniya kuma ya rasa N1.6 tiriliyan na kudinsa, a cewar Forbes
- Bernard Arnault, biloniya dan kasar Faransa, wanda iyalansa ne suka mallaki kamfanin kera kayayyakin nishadi ne ya sha gaban Musk
- Elon Musk ya rike kambun mai kudin duniya tun Satumban 2021, inda ya maye gurbin mai kamfanin Amazon Jeff Bezos
Mai kamfanin Tesla Elon Musk ya rasa matsayi na farko a jerin masu kudi na Forbes a ranar Laraba ga Bernard Arnault, wanda iyalinsa suka mallaki kamfanin LVMH, Daily Trust ta rahoto.
A yayin da darajan hannayen jari a Amurka suka fadi da tsoron fadawa matsin tattalin arziki, arzikin Musk ya ragu na dan lokaci kasa da na iyalan Arnault.
Amma misalin karfe 5.30 na yamma agogon GMT, Musk ya koma matsayinsa na daya da $184.9 biliyan yayin da Arnaul da iyalansa ke biye masa da $184.7 biliyan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Matsayin sauran attajiran duniya
A cewar rahoton Arise TV, Dan kasuwa na kasar Indiya Gautam Adani shine ke na uku da $134.8 biliyan, yayin da mai kamfanin Amazon Jeff Bezos shi kuma ya zo na hudu da $111.3 biliyan.
Arnault ya taba zama dan farko a jerin masu kudin duniya na Forbes na awanni a shekarar 2021.
Kamfaninsa na LVMH group, wacce ta kunshi kamfanoni da dama kamar Louis Vuitton, Givenchy, da Kenzo na cigaba da samun riba tare da bunkasa duk da halin da tattalin arzikin duniya ke ciki.
Musk, wanda galibin arzikinsa na kunshe ne da hannun jarin kamfanin Tesla, ya rika shiga 'rigingimu' tun bayan sayan kamfanin Twitter a watan Oktoban bara.
Ita ma kamfanin Bloomberg a kididdigan da ta yi ya nuna cewa Musk da Arnault suna kusa-kusa.
Fata-fata Kenan: Jama'a Sun Dauki Dumi Bayan Ganin Wani Kalan Takalmi Da Peter Obi Ya Sanya A Wurin Taro
Kididdigan Bloomberg, da aka kididdiga bayan rufe kasuwannin Amurka a ranar Talata ta nuna Musk ne ke kan gaba da $178.9 biliyan, sai Arnault ke biye da shi da $165.1 biliyan.
Bernard Arnault: Attajirin Da Ya Nemi Hambarar da Elon Musk a Matsayin Attajirin Duniya
Biyo bayan asarar Dalar Amurka biliyan 44 da Elon Musk ya yi a ranar Laraba 7 ga watan Disamba, Bernard Arnault ya zama attajirin duniya.
Amma daga bisani Arnault shine shugaban kamfanoni da dama ciki har da Louis Vuitton ya sauka daga wannan matsayi duk dai a ranar Laraban.
Asali: Legit.ng