An Bude Tsohon Babban Birnin Saudiyya, Ya Fi Shekaru 250 a Yadda Yake Tun Farko
- Kasar Saudiyya ta bude wani tsohon birninta domin ba masu sha’awar bude ido damar ziyarta da ganewa idanunsu ababen ban mamaki
- At-Turaif ne birnin da kasar Saudiyya ta fara kafa masarautarta, wurin da ke da masallatai, gidaje da fadojoji na ginin kasa
- Ana kyautata zaton wannan yunkuri zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasar ta fuskar kawo kudin shiga a fannin bude ido
Diriya, Saudiyya - A ranar 4 ga watan Disamba ne kasar Saudiyya ta bayyana bude wani tsohon birnin masarautar kasar mai suna At-Turaif.
Rahoton da muke samo ya bayyana cewa, At-Turaif ne babban masarautar Saudiyya na farko kafin zamanantar da kasar zuwa yadda take a yanzu,
BBC Hausa ta ce, za a bude birnin ne da ke yankin Diriya domin ba jama’a masu yawon bude ido damar dandana zakin tarihin farin masarautar kasar ta yanzu.
Kasar Saudiyya ta yi shirin yin hakan ne domin habakawa da farfado da garin wanda ya jima a tarihin kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa, At-Turaif gari ne mai dauke da fadoji da masallatai gami da na gidajen kasa da nan ne tushen sarautar Saudiyya tsawon shekaru 250 da suka gabata, Arab News ta ruwaito.
Abin da Saudiyya ke son cimmawa
Saudiyya na son cimma nasarar habaka birnin ne don ba masu yawon bude ido sha’awa kana don tuna tarihin kasar ga duniya.
A bangare guda, hakan zai habaka hanyoyin kudaden shiga na kasar ta hanyar masu bude a kasar.
Hakazalika, wannan birnin mai dimbin tarihi na cikin wuraren da aka ambata a matsayin masu dimbin tarihi a karkashin hukumar raya al’adu da majalisar dinkin duniya (UNESCO).
Akwai wurare da dama a duniya da suka shiga wannan kundi na hukumar UNESCO ko dai saboda dadewa da kayatarwa ko kuma sanuwarsu a duniya.
Saudiyya na cikin kasashen da ke tauye 'yancin addini, inji Amurka
A wani labarin kuma, kasar Amurka ta cire jerin sunayen kasashen da a imaninta suna tauye 'yancin addini ba kamar sauran kasashe ba.
Wannan na zuwa ne a cikin wani rahoton da kasar ta fitar, inda tace kasar Saudiyya na cikin wadannan kasashe.
Kasar Saudiyya na ci gaba da daidata lamurranta don ta yi kamanceceniya da sauran kasashen duniya don ba masu yawon bude ido sha'awa.
Asali: Legit.ng