Babban Rashi, A Yayin Da Tsohon Shugaban Kasa Mai Karfin Fada A Ji, Ya Mutu Yana Da Shekara 96
- Mutanen Jamhuriyar China sun shiga zaman makoki bayan rasuwar Jiang Zemin
- Jiang Zemin shine tsohon shugaban kasar China wanda ake yi wa kallon wanda ya jagoranci habbaka kasar ta zama yadda ta ke yanzu a karni na 21
- Ya rasu a yana da shekaru 96 a garin Shanghai bayan ya dade yana fama da ciwon leukaemia
Jiang Zemin, tsohon shugaban Jamhuriyar Mutane ta China, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Laraba 30 ga watan Nuwamba.
Wani rahoto da PM News ta wallafa, ya ce tsohon shugaban na China ya rasu a garin Shanghai yana da shekaru 96.
An sanar da rasuwarsa ne cikin wata sanarwa da Jam'iyyar Communist Party of China, da Standing Committee of the National People’s Congress of the People’s Republic of China (PRC), da the State Council of the PRC suka fitar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An mika sanarwar ne ga dukkan jam'iyyun siyasa, dukkan rundunar sojoji da kabilu baki daya da ke China.
Musababbin rasuwarsa
Kamar yadda Channels TV ta rahoto, tsohon shugaban kasar ya rasu ne sakamakon fama da cutar leukaemia da sassan jikinsa da suka dena aiki.
Shirye-shiryen da aka gabatar da gidajen talabijin na China ya nuna an saukar da tuta zuwa rabi a gidan gwamnati.
Ana alakanta Zemin da kawo cigaba a kasar a wannan karnin na 21.
An ce ya karbi mulki ne a 1989, ya kuma jagoranci kasar da ta fi kowanne kasa yawa a duniya har ta zama babban kasa mai karfin fada a aji a duniya.
Bayan murabus dinsa a shekarar 2003, China ta zama mamba a na kungiyar kasuwanci ta duniya. Bayan yan shekaru, China ta yi nasarar samun damar zama mai masaukin baki a wasar Olympic hakan ya kara karfafa ta tsakanin kasashe kamar Rasha, Amurka, Birtaniya da Jamus.
Allah ya yi wa kakakin majalisar dokokin Ekiti rasuwa
A wani rahoto, kun ji cewa Honarabul Funminiyi Afuye, kakakin majalisar dokokin jihar Ekiti, ya riga mu gidan gaskiya.
The Nation ta rahoto cewa Afuye, wanda ke wakiltar yankin Ikere ta 1 ya rasu ne yana da shekaru 66 a duniya a ranar 19 ga watan Oktoban 2022.
Asali: Legit.ng