Yadda Wani Mutum Ya Banka Wa Gidan Abinci Wuta Saboda An Yi Kuskure Wurin Kawo Masa Abin Da Ya Ke So

Yadda Wani Mutum Ya Banka Wa Gidan Abinci Wuta Saboda An Yi Kuskure Wurin Kawo Masa Abin Da Ya Ke So

  • Wani mutum a birnin New York ya gasgata karin maganan da ake cewa 'yunwa bata da hankali' bayan ya cinnawa gidan abinci wuta saboda kuskuren kawo masa abinci
  • Idan ka taba dandana 'chicken biryani' za ka gane dadin da abincin Swahili ke da shi, kuma wannan mutumin ya gaza sanin dalilin da yasa bai samu abin da ya ke so ba
  • Bayan kama Norbu, an kuma sake shi, hakan ya fusata yan sandan da suka dauki lokacin su suka kama mutumin

New York - Wani mutum mai suna Norbu, ya cinnawa gidan cin abinci wuta a birnin New York bayan an yi kuskuren kawo masa nau'in abinci 'chicken biryani'.

Ya yi odan a kawo masa 'chicken biryani' daga wani wurin cin abinci na yan Bangladeshi, amma lokacin da aka kawo masa wani abincin daban, ya fusata.

Kara karanta wannan

"Ba Bayan Gida, Babu Girki": Dan Najeriya Ya Gina Bandaki Mai Samar Da Iskar Das Don Girki Da Wutar Lantarki

Mutum yana cinna wuta
Wani Mutum Ya Kona Gidan Abinci Bayan An Kawo Masa Abinci Ba Wanda Ya Tambaya Ba, Hotuna Sun Fito. Hoto: New York Post.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar New York Post, mutumin ya amsa cewa yana cikin maye a lokacin da ya yi watsi da kudin.

Daga nan ya siyo gas ya cinnawa wurin cin abincin wuta, kuma ta kona takalminsa kamar yadda rahoto ya bayyana.

Mutumin da aka ce ya tsere daga wurin yayin da takalminsa ke ci da wuta ya ce:

"Na siyo tukunyar gas, na jefa cikin kantin na yi kokarin konawa. Na cinna masa wuta, kawai sai wutar ta kama ni."

Jami'an tsaro ba su ji dadin ganin an saki Norbu ba

Jami'an tsaro suna gunaguni ganin cewa an saki Norbu yana yawonsa a gari, suna cewa sun shafe kimanin sati biyu suna shan wahala kafin gano shi, kawai sai gashi an sake shi ba tare da beli ba.

Kara karanta wannan

Hotunan yadda matashi ke samar da wutar girki da ta lantarki daga toroso ya girgiza jama'a

Wata mai aiki a wurin sayar da abincin, amma, ta ce an bashi abincin da ya tambaya, amma ya watsa musu a fuska, Daily Mail ta rahoto.

Ma'aikaciya a wurin cin abincin ta ce:

"Ya bukaci a bashi chicken biriyani kuma mutanen da ke karbar oda suka kawo masa... Ya musu ihu yana cewa menene wannan, suka ce abin da ka ce a kawo, chicken biryani, kuma ya watsa musu a fuska!."

Masu bincike sun ce wutar ta lalata tagar gilashi na wurin cin abincin kuma ta lalata na'urar sanyaya wuri wato AC, an yi asarar dukiya ta fiye da KSh 181,800.

Bidiyon wani mutum da ya sauya baro zuwa babban kanti ya burge mutane

Mutane suna amfani da basira daban-daban wurin tallata hajarsu, hakan na sa wasu suna samun kasuwa.

Wani mai sayar da kayan wayoyin salula ya birge mutane ta yadda ya loda wa baro kaya tamkar kanti.

Kara karanta wannan

Abu Mai Sosa Zuciya: Hotunan Wani Matashi Bai Ci Abinci Ba Tsawon Kwana 2 ya Samu Taimako

A wani bidiyo da @aramite ya wallafa, an ga yadda mutumin ya cika baro makil da kayan wayoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164