An Daure Malamin Addini Adnan Oktar Bisa Laifukan Badala a Kasar Turkiyya

An Daure Malamin Addini Adnan Oktar Bisa Laifukan Badala a Kasar Turkiyya

  • Kotu a kasar Turkiyya ta yankewa Adnan Oktar mai da'awar shi malamin addinin Islama ne hukuncin zaman gidan kaso na shekaru sama da 8000
  • An kama Adnan da laifukan da suka shafi badala, kirkirar kungiyar asiri da dai sauran laifuka masu muni
  • A bara an yanke masa hukunci, amma ana daukaka kara, a jiya an sake yi masa hukunci mai tsawon gaske

Istanbul, Turkiyya - Wata kotu a Istanbul ta yanke daya daga hukuncin dauri mafi tsauri da tsawo a duniya kan wani malamin addini mai gabatar da shirye-shirye masu jawo cece-kuce a talabijin a Turkiyya, Adnan Oktar da aka fi sanu da Harun Yahya.

An yankewa Oktar hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 8,658 ne tare da wasu mutum 14 da ke tare dashi bisa laifukan da suka shafi tafiyar da haramtacciyar kungiya mai hadari.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Gargaɗi China: Ku Yi Taka Tsantsan Da Ba Wa Najeriya Bashi

A Janairun shekarar da ta gabata ne aka yankewa Oktar hukunci makamancin wanda aka yanke masa a jiya Laraba 16 ga watan Nuwamba, kamar yadda Bloomberg ta ruwaito.

Hukuncin jiya bai kai wanda aka yanke masa ba bara; na shekaru 9,803 da watanni shida, amma duk da haka hukuncin ya shiga jerin mafi tsawo a kasar Turkiyya da ma duniya baki daya.

An daure Adnan Oktar tsawon shekaru 8,658
An daure malamin addini Adnan Oktar bisa laifukan badala a kasar Turkiyya | Hoto: bloomberg.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda hukuncin bara ya kasance

Hukuncin da aka yanke masa bara dai kotun daukaka kara ya rushe shi tare da umartar a sake yin sa.

Hakazalika, kotun daukaka kara a lokacin ya saki mutum 68 da ake zargi tare da Oktar duba da jimawar zaman jiran shari'ar har sai an sake sanya lokacin zama, amma aka ci gaba da tsare Oktar da wasu makusantansa.

Hakazalika, masu shigar da kara sun rubuta bukatar sake dawo da mutum 61 zuwa magarkama. Kotu ta amince, an kamo mutum 50, aka sake gurfanar dasu a kotu a farkon 2022, rahoton Daily Sabah.

Kara karanta wannan

Satar N800m: An kama tsohon dan takarar gwamna yayin da yake shirin tserewa a Abuja

Hukuncin karshe na kotu

A ranar Labarar da ta gabata, kotu ta yi hukuncinta na karshe kan mutum 215, ciki har da 72 da ke tsare.

Hukuncin dai ya zo wa Oktar ba yadda yake zato ba, domin a baya yana kyautata zaton za a sake shi, amma reshe ya juya da mujiya.

An yanke masa hukuncin shekaru 891 ne bisa laifukan da suka shafi badala, tauye ilimin wasu, azabtar da wasu, satar mutane da kuma bin diddigi da adana bayanan jama'a ba tare da bin ka'ida ba.

Amma an ninka hukuncin Oktar ya zama shekaru 8,658 bayan da duba da cewa, dole ya dauki laifukan almajiransa da 'yan koronsa.

A watan Satumba, an zargi Oktar da wasu mutanensa da laifukan tafiyar da harkallar makamai da kuma tada hankali a lamarin addini. An kuma zarge su da tattara bayanan jama'a tare da bata musu suna.

Rahotonmu na baya ya bayyana yadda shari'ar ta 2021 ta kasance, kamar yadda rahotonni daga kasar ta Turkiyya suka bayyana.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.