Mai Kudin Da Yafi Dan Gote Kudi a Yana Da Shekara 30 Yanzu ya Zama Talaka

Mai Kudin Da Yafi Dan Gote Kudi a Yana Da Shekara 30 Yanzu ya Zama Talaka

  • Sam Bankman-Fried ya yi murabus a matsayin shugaban FTX yayin da kamfanin sa na crypto ya bayyana karyewar tattalin arziki
  • A 'yan watannin da suka gabata, Bankman-Fried ya kasance daya daga cikin manyan attajirai a duniya kuma ya kasance cikin manyan mutane 100 mafi arziki a duniya.
  • Dukiyar Bankman-Fried, a zahiri, ta fi ta Aliko Dangote, wanda ya fi kowa kudi a Afirka.

Sam Bankman-Fried, daya daga cikin attajirai mafi karancin shekaru a duniya, ya na da dukiyar da ta kai dala biliyan 26 (N11.4 tiriliyan a kudin Nigeria) daga watan takwas zuwa 11 ga Nuwamban shekarar da muke ciki

Babban hasarar da Bankman-Fried ya yi ya baiwa duniya mamaki kuma an dauketa wata asara mafi muni da wani mutum ya yi a tarihi.

A cikin watan Maris na 2022 wata mujalla mai suna Bloomberg ta sanya Bankman-Fried matsayi na biyar sama da Aliko Dangote, yayin da kuma mujallar Forbe ta sashi a cikin jerin masu kudin crypto.

Kara karanta wannan

Yadda Likitoci suka Cire Gurnet Da Ya Kusa Tashi Daga Kirjin Sojan Rasha, hotuna

Mai Kudin Duniya
Mai Kudin Da Yafi Dan Gote Kudi a Yana Da Shekara 30 Yanzu ya Zama Talaka Hoto: UCG
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga billionaire zuwa Talaka. Bankman-Fried ya shiga yanayi mafi muni bayan da dandalin cryptocurrency ya fadi, kuma FTX ya fada yanayin mashasharar tatalin arziki.

Sanarwar karyewar kamfanin ta zo ne bayan Bankman-Fried ya bar mukaminsa na Shugaban kamfani, wanda a halin yanzu baida ko sisi.

A 'yan watannin da suka gabata, arzikin Bankman-Fried ya karu zuwa sama da dala biliyan 26, kuma kamfaninsa, FTX ya kai dala biliyan 32 a karshen shekarar bara.

Koyaya, 'yan makonnin da suka gabata an ga darajar cryptocurrency ta faɗi sama da 20% yadda aka gani a asusun masu saka hannun jari.

Bankman-Fried ya mayar da martani ga Bankman-Fried ya wallafa wani sabuntawa a shafinsa na Twitter, wanda ya ce: "Wannan ba lallai ba ne ya zama yana nufin ƙarshen kamfanoni ko kuma ikonsu na samar da ƙima da kuɗi ga abokan cinikinsu musamman, kuma suna iya yin daidai da haka. sauran hanyoyin samar da kudi.

Kara karanta wannan

Yadda Wata Budurwa Yar Shekara 18 Ta Kashe Jaririnta Da Wuka Bisa Shawarar Mahaifiyarta Yar Shekara 60

Daga karshe ina da kwarin gwiwar cewa Mista Ray da sauransu za su iya taimakawa wajen samar da duk abin da ya fi kyau na bunkasa sabgar nan. "Na yi hakuri da gaske, kuma, cewa mun ƙare a nan. Da fatan, abubuwa za su iya kyau kuma mu farfado da kamfanin.
Zan yi aiki don fayyace inda abubuwa suke dangane da dawo da kawao da mai ido da wur-wuri.
Ina tattara dukkan bayanan, amma na yi mamakin ganin abubuwa sun bayyana yadda suka yi a farkon makon nan.
Ba da jimawa ba zan rubuta cikakken rubutu akan wasan kwaikwayo, amma ina so in tabbatar da cewa na samu daidai lokacin da ya kamata.
Hatsarin Crypto ya yi mana asarar arziki amma har yanzu muna da bege",

‘Yan kasuwar Najeriya sun koka

A wani rahoton Legit.ng ta fitar ya bayyana cewa, kasuwar hada-hadar kudi ta Bitcoin, ta yi hasarar kashi 52 cikin 100 na darajar ta tun lokacin da aka fara samun matsalar crypto a kasuwar duniya.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

Masana dai sun ce hadarin ya faru ne sakamakon koma bayan dalar Amurka da aka samu a wancan lokaci da kuma hauhawar farashin kayayyaki, lamarin da ya sa ‘yan kasuwa da dama suka fara hada-hadar sayar da su, lamarin da ya sa wasu da dama suka daina sa kudaden a ciki.

'Yan kasuwa da dama a Najeriya na kirga asarar da suka yi yayin da hadarin ya ci gaba da raguwa kuma darajar kasuwar Bitcoin ta kara faduwa cikin sauri.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida