Elon Musk Ya Kori Shugaban Tuwita Da Wasu Manyan Shugabanni 2 - Awanni Bayan Ya Siya Kamfanin

Elon Musk Ya Kori Shugaban Tuwita Da Wasu Manyan Shugabanni 2 - Awanni Bayan Ya Siya Kamfanin

  • Mai kamfanin Tesla Inc., Elon Musk ya sallami wasu manyan shugabannin Tuwita awanni bayan siye kamfanin
  • Wadanda Musk ya sallama sun hada da Parag Agrawal, shugaban Tuwita, Ned Segal, babban jami'in kudi; da Vijaya Gadde, babban lauyan kamfanin
  • Musk ya ce ya siya kamfanin ne ba don riba ba sai dai don ya bawa duniya damar samun dandali inda za a tattauna batutuwa ba tare da tashin hankali ba

Amurka - Elon Musk, biloniya kuma wanda ya kafa kamfanin Tesla Inc., ya sallami manyan shugabannin Twitter, The Cable ta rahoto.

Hakan na zuwa ne kasa da kwana guda bayan ya kammala cinikin siyan Tuwita, kuma bayan Musk ya yi alkawarin ba zai kori ma'aikata ba.

Kara karanta wannan

An tura N4.6bn wani asusu a mulkin Jonathan, EFCC ta fadi dalilin da yasa bata tuhume shi ba

Elon Musk
Elon Musk Ya Kori Shugaban Tuwita Da Wasu Manyan Shugabanni - Aawanni Bayan Siyan Kamfanin. @thecableng.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Manyan ma'aikatan da aka sallama

Wadanda aka sallama sun hada da; Parag Agrawal, shugaban Tuwita, Ned Segal, babban jami'in kudi; da Vijaya Gadde, babban lauyan kamfanin kuma shugaban tsare-tsare.

Dalilan korar shugabannnin na Tuwita

Gadde, daya daga cikin shugabannin, an ce an kore shi ne saboda babban rawar da ya taka wurin hana Donald Trump, tsohon shugaban kasar Amurka daga amfani da Tuwita.

A Janairun 2021, ta yi wa Trump dakatarwar dindindin daga amfani da dandalin, bayan magoya bayansa sun kai hari ginin majalisar Amurka.

Kamfanin ta ce ta yanke hukuncin ne bayan zanga-zangar ta ranar 6 ga watan Janairu 'don kare yiwuwar ingiza mutane su sake tada hankula.'

Da ya ke martani kan haramta masa amfani da Tuwita, Trump ya ce ba zai dawo ba koda an bude masa shafinsa, yana mai cewa zai tsaya a dandalin sada zumuntarsa ta Truth Social.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Jami’an Gwamnati 7 Da Shugaba Buhari Ya Tsige Daga Kujerunsu

Amma, a watan Mayu, sabon mammalakin na Tuwita, Musk, ya ce idan ya yi nasarar siyan Tuwita, zai janye haramcin da aka yi wa Trump.

A cewar biloniyan, kuskure ne 'haramtawa tsohon shugaban kasar amfani da shafin na dindindin.'

Abin da yasa na siya Tuwita - Musk

Bayan siyan kamfanin, Musk ya ce ya siya kafar saboda cigaban al'umma, ya kara da cewa hasashen da ake masa ba daidai bane.

Ya ce:

"Abin da yasa na siya Tuwita shine yana da muhimmanci ga cigaban duniya a samu zaure na tattaunawa a intanet ba tare da tada rikici ba. Akwai hatsarin cewa dandalin sada zumunta zai rabu tsakanin tsatsauran ra'ayi na hagu da dama hakan kuma zai kara raba kan al'umma da janyo kiyayya."

Attajirin Duniya, Elon Musk Ya Siya Twitter Kan Kuɗi Dalla Biliyan 44

Kamfanin Twitter, a ranar Litinin ta tabbatar da cewa za ta sayarwa attajirin duniya Elon Musk kan kudi Dallar Amurka Biliyan 44, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

Sayar da kamfanin abin mamaki ne duba da cewa da farko mambobin kwamitin kamfanin sun ki amincewa Musk ya siya kamfanin dandalin sadarwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164