Jerin Manyan Jami’an Gwamnati 7 Da Shugaba Buhari Ya Tsige Daga Kujerunsu
Akwai kariya sosai ta bangaren aiki a majalisar Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Da zaran an ba mutum mukami, ya kan shafe tsawon lokaci yana aiki harma a sabonta nadinsa idan har doka ta bayar da damar yin hakan.
Duk da haka, shugaban kasar ya sallami wasu yan tsirarun mutane da ya baiwa mukami a gwamnatinsa da ta yi sama da shekaru bakwai.
Na baya-baya cikin mutanen da aka sallama shine Effiong Okon Akwa, shugaban NDDC, wanda aka sallama nan take a ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba.
Ga jerin mutanen da shugaba Buhari ya sallama:
1. Saleh Mamman
An nada Saleh Mamman a matsayin ministan wutar lantarki jim kadan bayan tazarcen Buhari a 2019.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An sanar da sallamarsa a ranar Laraba, 1 ga watan Satumban 2021.
2. Sabo Nanono
An kuma sallami Sabo Nanono a matsayin ministan noma da raya kakkara a ranar 1, ga watan Satumban 2021.
An yi ta rade-radin cewa an tsige Mamman da Nanono ne saboda rashin kokari.
Sai dai fadar shugaban kasa ta karyata hakan inda ta ce Buhari ya dauki matakin ne don sake karfafa zangon karshe na mulkinsa.
3. Basheer Mohammed
A ranar 8 ga watan Satumban 2021, shugaba Buhari ya tsige Basheer Mohammed a matsayin darakta janar na hukumar NAPTIP.
Nan take shugaban kasar ya nada Fatima Waziri-Azi a matsayin sabuwar shugabar hukumar. Ba a bayyana dalilin sallamar nasa da shugaban kasar yayi ba.
4. Armstrong Idachaba
A watan Yunin 2021, Shugaba Buhari ya tsige Armstrong Idachaba a matsayin darakta janar na hukumar NBC.
An maye gurbin Idachaba da Balarabe Ilelah.
5. Farfesa Sani Mashi
A watan Maris 2021, shugaba Buhari ya tsige Farfesa Sani Mashi daga matsayin darakta janar na hukumar NIMET.
An maye gurbin Mashi, wanda wa'adin aikinsa ya kamata ya kare a ranar 22 ga watan Janairun 2022 da Farfesa Bako Mansur Matazu.
6. Kanal Milland Dixon Dikio mai ritaya
An tsige Kanal Milland Dixon Dikio mai ritaya daga matsayin shugaban ofishin kariya a Satumban 2022.
An maye gurbin Dikio da Manjo janar Barry Ndiomu mai ritaya.
7. Effiing Okon Akwa
Shugaba Buhari ya tsige shugaban hukumar ci gaban Neja Delta (NDDC), Effiong Okon Akwa, nan take daga rabar Alhamis, 20 ga watan Oktoba.
An sanar da batun sallamar Akwa a cikin wata sanarwa daga daraktan labarai na ma'aikatan harkokin Neja Delta, Patricia Doritshe.
2023: Kar Ku Yi Danasani da Mulkin Buhari, Tinubu Ga Yan Najeriya
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bukaci yan Najeriya da kada su yi danasani kan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tinubu ya ce kada su bari masu adawa su yaudare su cewa shugaban kasar bai tabuka komai ba tsawon shekaru bakwai da ya yi kan karagar mulki.
Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya yi jawabi ne a Kano yayin kaddamar da ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a jihar.
Asali: Legit.ng