An Yanke Hukuncin Daurin Rai Da Rai Ga Matar Da Ta Hada Baki Da Saurayi Don Kashe Mijinta, Su Ci Dukiya Tare
- Kotu a Kasar Korea ta Kudu ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wata mata Lee Eun-hae saboda kashe mijinta
- Kotun ta kuma yankewa saurayin Lee, mai suna Cho Hyun-soo, daurin shekaru 30 a gidan gyaran hali saboda hadin baki wurin kashe mijin Lee
- Binciken ya nuna wadanda aka yanke wa hukuncin sun taba yunkurin kashe mijin a baya har sau biyu sun su karbi kudin inshoran rai
Koriya Ta Kudu - Wata kotu a ranar Alhamis ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan wata mata da aka gurfanar kan nutsar da mijinta a ruwa a 2019 don samun makuden kudi na inshoran ransa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi wa saurin daurin shekaru 30 a gidan yari
Abokin hadin bakinta kuma saurayinta shi kuma an yanke masa daurin shekaru 30 a gidan yari, NAN ta rahoto.
Kotun yankin Incheon ta yanke wa Lee Eun-hae, yar shekara 31 da masoyinta, Cho Hyun-soo, dan shekara 30 hukuncin tare da bukatar su saka na'urar lantarki da zai rika nuna inda suke tsawon shekaru 20.
An yanke wa mutanen biyu hukuncin ne saboda ingiza mijin matar dan shekara 39 ya yi tsalle cikin rafi mai zurfi a Gapyeong, a Yunin 2019, duk da sun san cewa bai iya ninkaya ba, suka kyalle shi ya nutse.
Sau biyu suna yunkurin kashe mijin ba su yi nasara ba
An kuma zargi mutanen biyu da yunkurin kashe mijin ta hanyar bashi gubar kifi mai suna puffer a watan Fabrairu da kokarin nutsar da shi a wurin su a watan Mayu.
Masu gabatar da kara, a farko sun nemi kotu ta yanke wa mutanen biyu daurin rai da rai, saboda sun shirya aikata laifin ne don samun dallar Amurka miliyan 800 a matsayin inshora da za a biya bayan mutuwar mijin Lee.
Kotun ba ta yarda da masu shigar da karar ba na cewa masu laifin sun 'ingiza' mijin ya shiga rafin, sai dai laifinsu shine kin taimaka masa lokacin da suka ga ya nutse.
Kotun ta ce:
"A yunkurin neman samun kudin inshoran rai na miliyan 800, sun yi yunkurin kashe wanda abin ya faru da shi sau biyu amma ba su yi nasara ba, suka ki fasawa har sai da suka yi nasara.
"Daga binciken farko, wadanda ake zargin sunyi kokarin rufe laifukansu kuma ba su nuna nadama ba ko tuba."
An Yanke Wa Korarren Ɗan Sandan Najeriya Ɗaurin Rai Da Rai A Legas
A wani rahoton, wata babban kotun Jihar Legas, a ranar Juma'a 23 ga watan Satumba, ta yanke wa wani korarren dan sanda Olalekan Ogunyemi, daurin rai dai rai saboda kashe wani mai wanda ya zo kallon kwallon kafa, Kolade Johnson, Daily Trust ta rahoto.
Ogunyemi, wanda ke aiki tare da tawagar yaki da yan kungiyar asiri na yan sanda, ya bindige Johnson a cikinsu a ranar 31 ga watan Maris na 2019 a wurin kallon kwallo a Mangoro, Ikeja, Legas.
Asali: Legit.ng