Rishi Sunak Ya Zama Sabon Firayim Ministan Kasar Birtaniya

Rishi Sunak Ya Zama Sabon Firayim Ministan Kasar Birtaniya

  • An zabi Rishi Sunak a matsayin sabon firayam minista na Birtaniya bayan samun goyon bayan yan majalisa fiye da 100, idan aka kwatanta da abokin hamayyarsa, Penny Mordaunt
  • Sunak dan siyasa ne dan shekaru 42 dan Birtaniya-Asia kuma daya daga cikin attajirai a Westminster zai kafa sabuwar gwamnati tare da Sarki Charles
  • Tsohon kansilar zai karbi mulki ne daga Liz Truss ya ceto kasar daga matsalolin tattalin arziki da ta tsinci kanta da ya tura mutane da dama cikin talauci

Birtaniya - Rishi Sunak ya zama sabon shugaban jam'iyyar United Kingdom's Conservative Party a Birtaniya, The Punch ta rahoto

A cewar sanarwa da Sir Graham Brady ya fitar, kwamitin 1922 sunan mutum daya kawai ta samu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar, kuma ya samu goyon bayan yan majalisa guda 100.

Kara karanta wannan

Bako cinye gida: Kadan daga tarihin sabon Firayinministan Burtaniya Rishi Sunak

Sunak
Rishi Sunak Ya Zama Sabon Farayim Ministan Birtaniya. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Don haka, Sir Brady, ya ayyana cewa Sunak shine zai sama sabon shugaban jam'iyyar kuma daga baya sabon firayim Minista.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya tabbatar cewa sabon shugaban na Tory, Rishi Sunak zai yi wa yan majalisar jawabi misalin karfe 14.30 BST.

Yanzu nauyin da ya rataya a kansa shine na jagorantar kasar ta fito daga matsalar tattalin arziki da ta shiga.

Wanene Rishi Sunak?

Matashin firayim ministan yana daya daga cikin yan siyasa mafi arziki a Westminster, kuma an sa ran zai kafa gwamnati tare da Sarki Charles, ya maye gurbin Liz Truss, firayim minista mai barin gado wacce ta shafe kwanaki 44 kacal a ofis.

An yi wa Sunak maraba da tafi da buga tebura a yayin da ya iso zauren majalisa don yin jawabi ga yan majalisar bayan sanar da sakamakon zaben.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Wike Ya Fallasa Abinda Atiku Ya Masa a Ribas, Yace Ba Zai Masa Kamfen Ba a 2023

Tsohon kansilar ya samu goyon bayan fiye da rabin yan majalisa, yayin da abokin hamayarsa, Penny Mordaunt, bai yi nasaran samun goyon baya daga yan majalisar ba.

Mutane nawa suka kada wa Rishi Sunak kuri'a?

Mordaunt ta janye daga takarar yan mintuna kafin a sanar da wanda ya yi nasara.

Ta ce:

"Wannan shawarar ta kasance mai tarihi kuma ta sake nuna cewa jam'iyyar mu na maraba da kowa da baiwar da muke da shi. Na bawa Rishi cikakken goyon baya na."

Zai zama firayim minista na farko wanda asalin iyayensa yan Indiya ne.

Kafin yanzu, Labour ta dade tana kira a yi babban zabe.

Truss, Sabuwar Firayim Ministan Ingila Tayi Murabus

Tunda farko kun ji cewa, Firayim ministan Ingila, Liz Truss, a ranar Alhamis tayi murabus daga mukaminta kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Wannan murabus din ba zuwa ne kasa da watanni biyu da hawanta kujerar ta.

Truss wacce ta kwashe kwanaki 45 a ofis tace tayi murabus ne bayan mako daya da tayi neman wanda zai gaje ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164