Jirgin Sama Dauke da Fasinjojin Ya Bace Bat a Sararin Samaniya

Jirgin Sama Dauke da Fasinjojin Ya Bace Bat a Sararin Samaniya

  • Wani jirgin sama mai zaman kansa da ya ɗauko mutum 5 yan kasar Jamus ya ɓata a sararin samaniya bayan taso wa daga Mexico
  • Ma'aikatar tsaro ta ƙasar Costa Rica, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace Jirgin ya nufi gabashin ƙasar ne kafin ya ɓata
  • Ministan tsaron kasar, Jorge Torres, yace zasu yi duk me yuwuwa don gano inda Jirgin ya yi

Wani rahoto da muka samu daga ƙasar Costa Rica ya nuna cewa wani Jirgin Sama da ya ɗakko fasinjoji ya ɓace a Sararin samaniya jim kaɗan bayan tashinsa.

Jaridar Aminiya watau sashin Hausa na Daily Trust ta tattara cewa Jirgin wanda ya ɗauko fasinjoji biyar yan ƙasar Jamus ya bata ne da misalin karfe 12:00 na tsakar dare a Agogon GMT.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

Jirgin Sama.
Jirgin Sama Dauke da Fasinjojin Ya Bace Bat a Sararin Samaniya Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Ma'aikatar tsaro ta ƙasar Costa Rica ta tabbatar da cewa Jirgin ya ɓata ne ba'a san inda yake ba da tsakar dare gabanin wayewar garin ranar Asabar data gabata.

Ministan tsaron ƙasar, Jorge Torres, yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun samu labarin ɓacewar wani Jirgin Sama mai zaman kansa wanda ya ta so daga kasar Mexico zuwa yankin Lardin Lemon dake gabashin Costa Rica."
"Jirgin na ɗauke da yan kasar Jamus guda 5. An daina jin duriyar jirgin ne yayin da sadarwa ta katse a kewayen turken sadarwa da ke La Barra de Parismina a Costa Rican Caribbean.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Ministan ya ci gaba da cewa, "Ba tare da ɓata lokaci ba (bayan rasa sadarwa da jirgin) muka ɗauki muhimman matakan da suka dace da nufin ceto Jirgin saman."

Bugu da kari, Yace rashin kyaun yanayi ya sa tilas suka dakatar da aikin zakulo jirgin da dare, amma ya ba da tabbacin zasu ci gaba da safiyar Asabar.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Abokin Atiku Ya Yi Watsi Da Shi, Ya Faɗi Ɗan Takarar Da Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

A wani labarin kuma Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su

Dan kwallon kafa a Bayelsa, Earnest Peremobowei, ya riga mu gidan gaskiya sakamakon nutsewa da ya yi cikin ruwa bayan ya ceto wasu mutane guda biyar.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin dan shekara 31 yana kan hanyarsa ne na zuwa Yenebelebiri tare da wasu mutane biyar don zuwa su duba gidajensu da ambakiyar ruwa ta cinye amma jirgin ya yi hatsari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262