Bidiyon Matashin da Ya Hadu da Mahaifiyarsa Karo na Farko Bayan Shekaru 30 da Rabuwarta da Mahaifinsa

Bidiyon Matashin da Ya Hadu da Mahaifiyarsa Karo na Farko Bayan Shekaru 30 da Rabuwarta da Mahaifinsa

  • Wani bidiyo mai taba zuciya ya nuna lokacin da wani matashi ya sake ganawa da mahaifiyarsa bayan shekaru 30 da rabashi da ita
  • Mutumin mai suna Abdullahi Khojali ya rushe da kuka yayin sake haduwar wacce tayi matukar bashi mamaki
  • Iyayensa sun rabu jim kadan bayan haihuwarsa, daga nan ne ya koma karkashin kulawar kakarsa a Saudi Arebiya

Wani matashi da ya tashi karkashin kulawar mahaifiyar babansa, ya sake ganawa da mahaifiyarsa bayan shekaru 30 da rabuwarsu.

Abdallah
Bidiyon Matashin da Ya Hadu da Mahaifiyarsa Karo na Farko Bayan Shekaru 30 da Rabuwarta da Mahaifinsa. Hoto daga @ilmfeed
Asali: Instagram

Wani bidiyo ya nuna yadda Abdullah Khojali yayi girma sosai, gami da fashewa da kuka a lokacin da mahaifiyar tasa ta shigo cikin dakin don haduwa dashi ba tare da sanarwa ba.

Abdullah Khojali ya hadu da mahaifiyarsa a karo na farko a shekarar 2014, shekaru 30 bayan rabuwarsu.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet, Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

Abdullah, wanda a halin yanzu ya kasance kwararren ‘dan kwallon kafa ne bai sake ganin mahaifiyarsa ba bayan da suka rabu da mahaifinsa, shekaru 30 da suka gabata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abdullah Khajoli bai taba sanin cewa mahaifiyarsa na raye ba

Mahaifiyarsa ‘yar asalin Sudan ce. Bai san cewa tana raye ba har sai da ya kai shekaru 15 a duniya bayan kakarsa ta sanar masa.

Ya dinga kokarin ganin ya gano inda take amma hakan bai yuwu ba har sai shekarar 2014 yayin da suka yi wata haduwar ba-zata.

An nadi bidiyon a 2014 amma sai shekarar 2022 ne aka yada shi.

Kalla bidiyon:

Soshiyal midiya tayi

@usamashoaib01 yace:

“Allah ya ba wa iyayenmu mata rayuwa doguwa mai cike da lafiya.”

@fizahnur tayi tsokaci da:

“Ba zan iya kwatanta a raba uwa da ‘Dan ta ba na tsawon shekaru 30.”

Kara karanta wannan

Mace Ba Yar Goyo Bace: Bakano Ya Je Shagalin Auren Aminsa, Ya Gano Budurwarsa Ce Amaryar

@bahaar-e-zindagii yace:

“Sun saka ni kuka da sassafen nan. Iyayena sun rasu. Ban cika maganarsu ba saboda ina kewarsu. Ya Allah ka tsawaita rayuwar iyayen kowa kuma ka basu babban masauki a jannatul Firdausi.”

@falak7fatima tace:

“Ya Allah, wannan zalunci ne a raba uwa da Dan ta na tsawon shekaru. Bai dace mahaifi yayi hakan ba.”

Hatta Mijina Yana Alfahari dani: Mahaifiyar Yara 2 Direban Tasi Ta Birge Jama’a a Bidiyo

A wani labari na daban, Matar aure kuma mahaifiyar yara biyu wacce direban tasi ce wacce ta shawarci sauran mata da kada su saki jiki ba tare da neman na kansu ba.

Kemi Toriola wacce mahaifiyar yara biyu ce ta shiga sana’ar tukin tasi bayan annobar COVID-19 ya yi matukar illa ga kasuwancinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel