Jerin Kananan Yara 10 Mafi Arziki a Duniya, Shekarunsu, Dukiyar da Suka Mallaka da Iyayensu
- Wasu shahararrun yara masu arziki suna tara dukiyarsu ne da guminsu yayin da wasu kan samu nasu ne ta hanyar gada daga iyayensu
- Mafi kankanta a cikin yaran shekarunsa 4 a duniya, kuma babban cikinsu shekarunsa 17, sun tara kudinsu ne ta hanyar aiki tukuru
- Wasu daga cikin yaran sun kasance ‘ya’yan manyan mutane wadanda sune suka tara masu wadannan dukiya
Ba manya bane kadai suke tara arziki kuma basu kadai bane darajar dukiyoyinsu ke kaiwa biliyoyin kudi.
Wasu yaran ma suna rike da nasu arzikin kuma darajar dukiyoyinsu ya kai matakin biliyoyi kama daga kadarori zuwa tsabar kudi.
Yayin da wasu suka samu kudinsu ta hanyar gada daga iyayensu masu arziki, wasu sun samu arzikinsu ne da guminsu.
True Thompson (shekaru 4): Dala miliyan 5
True Thompson sunanta ne na karshe a jerin kuma ta kasance diya ga shahararriya jaruma Khloé Kardashian da shahararren dan wasan kwallon raga na kasar Kanada, Tristan Thompson.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Suri Cruise (shekaru 16) Dala miliyan 5
Suri Cruise mai shekaru 16 ta kasance diya ga jarumi Tom Cruise da jaruma Katie Holmes. Ta kasance yar kwalliya, ita ta zo ta 21 a cikin zaben mata mafi iya sa kaya a duniya lokacin da take shekaru 5.
Alina Morse (shekaru 17) Dala miliyan 6
Alina Morse ta kasance miloniya wacce ita ta gina kanta kuma ta shiga jerin yara marfi arziki. Ta kasance yar kasuwa kuma shugabar Zolli Candy, wani kamfanin yin alawa wanda ta kafa tana da shekaru tara a duniya.
Ryan Guan (shekaru 10) Dala miliyan 11
Ryan Guan ya kasance shahararre a dandalin YouTube da tasharsa mai suna Ryan’s World, an fi saninsa da Ryan’s Toys. Shafinsa yana bitar wasanni wanda ke nuno shi tare da iyayensa da tagwayen kannensa.
Budurwa Mai Shekaru 92 da Bata Taba Soyayya ba ko Aure Ta Bayyana Babbar Nadamarta a Bidiyo Mai Taba Zuciya
Valentina Paloma Pinault (shekaru 14) Dala miliyan 12
Valentina Paloma Pinault ta kasance diyar shahararriyar jaruma Salma Hayek da babban dan kasuwan Faransa Francois-Henri Pinault. Valentina ta samu shiga jerin yara masu arziki a duniya a 2020 da 2022.
Prince Louise na Cambridge (shekaru 4) Dala miliyan 400
Prince Louis, shine na uku kuma karamin dan Prince William da Catherine, Shine na 5 a cikin magadan sarautar Ingila bayan kakansa, mahaifinsa, babban wanda da kanwarsa.
Stormi Webster (shekaru 4) Dala miliyan 726
Stormi Webster ta kasance Kylie Jenner da Travis Scott mai shekaru 4, ta yi suna sosai a kan dukiyar da ta kai sama da dala miliyan dari bakwai wanda take bin biloniyan iyayenta.
Blue Ivy Carter (shekaru 10) Dala biliyan 1
Blue Ivy Carter ta kasance mawakiyar Amurka kuma diya ga shahararrun mawaka Beyoncé da Jay-Z. Ta zama shahararriyar yarinya a duniya kwanaki biyu bayan haihuwarta, a cewar Time.
Ci gaba: Najeriya ta samu karuwa, Buhari ya ba Turawa da 'yan wasu kasashe shaidar zama 'yan Najeriya
Prince George na Cambridge (shekaru 8) Dala biliyan 3
Yaro mafi arziki na biyu kuma dan gidan sarautar Ingila. Shakka babu, dukiyarsa ta samo asali ne daga gidan sarautar; da shekaru 8, arzikinsa ya kai sama da dala biliyan 3.
Princess Charlotte: Dala biliyan 5
A cewar rahotanni, Princess Charlotte ce yarinya mafi arziki a duniya. Ta kasance yar gidan sarautar Ingila kuma ta biyu sannan diya mace daya tilo da Prince William da charlotte suka mallaka.
Jerin Sunayen Yan Siyasar Najeriya Da Suka Mallaki Fitattun Jaridu Da Tashoshin Talbijin
A wani labarin, mun ji cewa wasu manyan yan siyasar Najeriya sun mallaki wasu manyan kafofin watsa labarai, inda a wasu gabar yake kasancewa rade-radi.
Sai dai kuma a wannan shafin, Legit.ng ta binciko zahirin gaskiya inda ta tattaro jerin wasu manyan yan siyasa a kasar wadanda suka zuba jari sannan suke kama kudi a bangaren jarida.
Asali: Legit.ng