Jerin Kadarorin da Sarauniya Elizabeth II Ta Bar wa Yarima Charles da Kimarsu

Jerin Kadarorin da Sarauniya Elizabeth II Ta Bar wa Yarima Charles da Kimarsu

  • Ba sabon labari bane, sarauniya Elizabeth ta mutu kuma tabbas ta bar tarin dukiya mai yawa da ta hada da kayan ado na alatu, zane-zane masu kayatarwa, gidaje da sauran kadarori
  • An ce sarauniya bata da takammamen albashi na wata-wata sai dai tsayayyen kudin da take samu na shekara wanda ya kai miliyoyin fam da yawa
  • Rahotanni sun ce sarauniyar ta bar wa danta Yarima Charles III gadon zunzurutun kudi kimanin dala miliyan 70 ya zuwa mutuwarta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sarauniya Elizabeth II ta rasu a jiya Alhamis 8 ga watan Satumban 2022. Ta shekara 96 kafin Allah ya karbi ranta a gidanta dake Scotland.

Ta bar tarin dukiya mai yawa da aka ce ta kai sama da dala miliyan 500, wanda kuma danta Yarima Charles ne zai gada ya ci gaba da cin duniyarsa da tsinke.

Kara karanta wannan

Shugaban wata kasa mai karfin iko ya ce ba zai halarci bikin bison sarauniyar Ingila ba

Kadarorin da sarauniya Elizabeth ta barwa danta
Jerin Kadarorin da Sarauniya Elizabeth II Ta Bar Wa Yarima Charles da Kimarsu | Hoto: ndtvimg.com
Asali: UGC

Dalla-dalla: Dukiyar sarauniya Elizabeth da abin da ta bari

A cewar wani rahoto na Fortunes, mafi yawan kadarorin sarauniyar mallaki ne na Royal Firm, ciki har da dala biliyan 28 na gidan sarautar Burtaniya da Sarki George VI da Yarima Philip suka ambata a matsayin kasuwancin ahali.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarauniyar na samun kudaden shiga ne ta asusun biyan haraji da ake kira Sovereign Grant, wanda ake ba dangin masarautar Burtaniya a duk shekara.

Hakan ya samo asali daga wata yarjejeniya da Sarki George III ya yi na daina karbar kudin wata-wata daga majalisa don yake karba duk shekara saboda kyautata goben ahalin gidan sarautar.

A farko ana kiran wadannan kudade da ake ba masarautar da Civil List, amma daga baya aka sauya sunan zuwa Sovereign Grant a shekarar 2012.

Hanyar da ake bi wajen biyan sarauniya

Kara karanta wannan

Jerin Kasashen Afirka 10 Da Suka Samu Yancinsu A Zamanin Mulkin Sarauniya Elizabeth II

Rahotanni sun ce, kudin da aka tarawa sarauniya a karkashin Sovereign Grant a tsakanin shekarun 2021 zuwa 2022 sun dala miliyan 86.

Kudaden dai na tafiye-tafiyenta ne, tara kadarori, kula da aikatace-aikace da dai sauran lamurran gidan sarauta.

The Royal Firm, kamfanin da kuma aka sani da Monarchy Plc, ya kunshi gungun manyan membobi da manyan jiga-jigai a House of Windsor.

Kadan daga abubuwan da ta bari inji rahoton Forbes sun hada da:

  1. The Crown Estate: $19.5bn
  2. Buckingham Palace: $4.9bn
  3. The Duchy of Cornwall: $1.3bn
  4. The Duchy of Lancaster: $748m
  5. Kensington Palace: $630m
  6. The Crown Estate of Scotland: $592m

Shugaba Putin Ba Zai Halarci Jana’izar Sarauniya Elizabeth Ba, inji Dmitry Peskov

A wani labarin, shugaban Vladimir Putin na kasar Rasha bai yi shirin halartar jana'izar Sarauniya Elizabeth II ba, in ji mai magana da yawunsa Dmitry Peskov a wani taron manema labarai a yau Juma'a 9 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Hoto: Mahaifiya Ta Yi Dambe Da Damisa Da Ya Yi Yunkurin Halaka Danta

Duk da cewa Rasha na mutunta ta saboda hikimarta, shugaba Putin ba zai halarci bikin ba kamar yadda Peskov ya bayyanawa manema labarai, Punch ta ruwaito.

Rahotanni daga kasashen duniya da dama sun mika sakon ta'aziyya ga murnar nadin saraunta ga sabon sarkin Ingila Charles III.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.