Twitter Ya Goge Rubutun Wata Farfesar Najeriya da Ta Yiwa Sarauniyar Ingila Fatan Mutuwa Mai Radadi
- Awanni kadan kafin mutuwar sarauniyar Ingila, wata mata 'yar Najeriya ta jawo cece-kuce a shafin Twitter
- Farfesa Anya, wata 'yar Najeriya da ke zaune a Amurka ta yiwa sarauniya addu'ar mutuwa mai radadi
- Kamfanin Twitter ya fusata, ya goge rubutun da farfesar ta yi tare da bayyana hakan a matsayin abin da ya saba doka
Kamfanin Twitter ya goge wani rubutun farfesa Uju Anya, malama a jami’ar Carnegie Mellon ta Amurka, kan martaninta ga rashin lafiyar Sarauniyar Ingila Elizabeth II.
Twitter ya goge rubutun ne sa'o'i kadan bayan buga shi a ranar Alhamis 8 ga watan Satumba.
A cewar Twitter:
"Wannan rubutu ya saba ka'idojin Twitter."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda batun ya soma tsakanin Twitter da farfesar
'Yan sa'o'i kadan kafin rasuwar sarauniyar, farfesa Anya ta yi wasu lafuzza masu sukar sarauniyar a shafinta Twitter, inda ya yi mata fatan mutuwa mai radadi.
Matar 'yar asalin Najeriya da ke zama a Amurka ta zargi marigayiya sarauniyar Ingila da kitsa “kisan kare dangi”, lamarin da tace ya kai ga 'dai'daita danginta.
Rubutun wannan farfesa dai bai yyiwa jama'a da dama dadi ba, wannan yasa aka samu yawaitar martani daga mutane daban-daban.
Jeff Bezos, mu'assasin kamfani kuma kantin zamani na Amazon na daya daga cikin wadanda suka fusata, kuma ya yi martani mai zafi.
A bangare guda, jami'ar da take aiki a Amurka ta yi Allah wadai tare da nesanta kanta da wannan batu da suka ce ya yi tsauri da yawa.
Hakazalika, jami'ar ta ce ba halinta bane goyon byanan irin wadannan maganganu masu tada tarzoma.
Sarauniyar Ingila, Elizabeth II Ta Kwanta Da, Ta Rasu Tana da Shekaru 96
A wani labarin, yanzu muke samun labarin rasuwar sarauniyar Ingila Elizabeth II bayan 'yar gajiriyar rashin lafiya da aka sanar ta yi a yau Alhamis 8 ga watan Satumba.
Rahotanni daga majiyoyi sun shaida cewa, masarautar Ingila ta tashi bakin labarin jirkicewar lafiyar sarauniya, lamarin da yasa likitoci ke kai komo a kanta.
A wata sanarwar da masarautar ta Ingila ta fitar, an sanar da rasuwar sarauniyar da yammacin Alhamis.
Asali: Legit.ng