Da Dumi-dumi: Sarauniyar Ingila Na Gab Da Shekawa Barzahu, Likitoci Sun Fadi Mafita

Da Dumi-dumi: Sarauniyar Ingila Na Gab Da Shekawa Barzahu, Likitoci Sun Fadi Mafita

  • An shiga halin tsoro da damuwa sosai kan halin da lafiyar Sarauniyar Ingila, Elizabeth ke ciki
  • A halin yanzu, likitocin Elizabeth sun bayar da shawarar sanya ido sosai a kan lafiyarta a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumba
  • Tuni makusantanta Sarauniyar mai shekaru 96 suka fara isowa gidanta da ke fadar Balmoral

Ingila - Likitoci sun shiga damuwa kan rashin lafiyar Sarauniya Elizabeth ta kasar Ingila, kuma sun bayar da shawarar sanya idanu sosai kan tsohuwar mai shekaru 96.

Fadar Buckingham ce ta bayar da wannan sanarwar a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumba, kuma ta ce shakikanta za su kasance a tare da ita.

Sarauniyar ta Ingila mafi dadewa a kan karagar mulki kuma basarakiya mafi tsufa a duniya tana fama da rashin lafiya tun a karshen shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

Sarauniyar Ingila
Sarauniyar Ingila Na Gab Da Shekawa Barzahu, Likitoci Sun Fadi Mafita Hoto: @FalklandsRepUK
Asali: Twitter

Tun daga lokacin aka datse fitowarta a taron jama’a kuma a ranar Laraba, an soke taron majalisarta na intanet wanda aka shirya yi tare da wasu manyan ministoci bayan likitocinta sun bayar da shawarar cewa ta huta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar Talata ne Sarauniya ta nada Liz Truss a matsayin sabuwar Firaministar Birtaniya a gidanta na Scotlan da ke fadar Balmoral.

Kmar yadda sashin BBC ya rahoto, sanarwar ta ce:

“Bayan sake dubata a safiyar yau, likitocin sarauniyar sun damu da yanayin lafiyar Mai martaba kuma sun bayar da shawarar ta ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar likitoci.
“Sarauniya tana samun sauki a Balmoral.
Yarima Charles da jikanta Yarima William a yanzu suna tare da ita. Hakazalika surukarta Duchess na Cornwall ita ma ta tafi Balomral ."

Har ilay yau, sashin Hausa na BBC ya rahoto cewa Firaminista Liz Truss ta ce dukkan al’ummar Ingila na cikin damuwa da jin labarin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Damke Tukur Mamu, mai sulhu tsakanin yan bindiga da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna A Kasar Misra

Ta kara da cewa:

"Addu’ata da ta dukkan al’ummar Birtaniya na tare da Ranta ya daɗe Sarauniya tare da iyalanta a wannan lokaci."

Shekaru 70 kan karagar mulki: Sarauniyar Ingila ta kafa tarihin da aka jima ba’a gani ba

A wani labarin, mun kawo cewa a ranar 6 ga watan Fabrairun bana ne Sarauniya Elizabeth II ta cika shekaru 70 a kan karagar mulkin Burtaniya.

Jaridar New York Times ta ba da rahoton cewa wannan ci gaba ya sanya sarauniyar cikin rukunin da ba a cika gani ba a tarihi, inda tarihi ya rubuta cewa, wasu sarakuna uku ne kawai aka san sun yi mulki sama da shekaru 70.

Kafar labarai ta CNN ta kara da cewa Elizabeth II, mai shekaru 95, ta zama sarauniyar Burtaniya ne bayan rasuwar mahaifinta King George VI a ranar 6 ga Fabrairu, 1952, yayin da take kasar Kenya a wani rangadi na kasa da kasa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Fitacciyar 'Yar TikTok Tana Girgijewa a Masallaci, 'Yan Sanda Sun Kama ta

Asali: Legit.ng

Online view pixel