Takaitattun Bayanan da Ya Kamata Ku Sani Game da Marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth II
A yammacin yau Alhamis ne masarautar Ingila ta sanar da rasuwar sarauniya mai dogon zamani, Elizabeth II bayan shafe shekaru sama da 70 a kan karagar mulki.
Bari mu yi waiwaye zuwa kadan daga tarihinta, da kuma irin tasirin da take dashi a idon duniya ba ma a iya masarautar Ingila kadai ba.
1. Haihuwarta da nasabarta
Sarauniyar Ingila da aka fi sani da Elizabeth II, cikakken sunanta shi ne; Elizabeth Alexandra Mary kuma an haife ta ne a ranar 21 ga watan Afrilun 1926 a Mayfair, Yammacin birnin Landan a kasar Burtaniya.
Mahaifinta shi ne sarkin Ingila na wancan lokacin, Sarki George VI da ya rasu a 1952. Mahaifiyarta kuwa ita ce Elizabeth Angela Marguerite Bowes-Lyon.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tana kanwa daya tilo da ake kira Gimbiya Margaret, wacce aka haifa a 1930, kamar yadda littatafan tarihi suka tabbatar.
2. Aurenta da Yarima Phillip
Sarauniya ta gamu da farin cikin rayuwarta Yarima Phillip na Kirka da Denmark a shekarar 1934, kana suka sake gamuwa 1937. Su duka dangi ne mai karfi ta tsatson Sarauniya Victoria da kuma dangi mai dan nisa da Sarki Christian IX na Denmark.
Tana da shekaru 13 ta alanta kamuwa da soyayyar Yarima Phillip daga nana aka yi baikonsu tana da shekaru 21.
A ranar 20 ga watan Nuwamban 1947 Sarauniya Elizabeth ta amarce da Yarima Phillip a wani kasaitaccen biki.
3. Haihuwa da yawan 'ya'yanta
A ranar 14 ga watan Nuwamban 1948 ta haifi danta na fari, wato Yarima Charles. Sun haifi diyarsu ta biyu; Gimbiya Anne, a ranar 15 ga watan Agustan 1950.
Ta haifi dan ta na uku, Yarima Andrew, a ranar 19 ga watan Fabrairun 1960. Shekaru hudu bayan haka, ta haifi dan ta na hudu, Yarima Edward, a ranar 10 ga watan Maris din 1964.
4. Hawanta sarauta
Mahaifinta ya fara rashin lafiya a 1951, lamarin da ya boye sarkin na Ingila a wancan lokacin ga taruka da dama da ma fita bainar jama'a.
A farkon shekarar 1952, Elizabeth da Philip sun fita rangadi zuwa kasar Australia da New Zealand ta za kuma su ratsa ta Kenya.
Jim kadan bayan dirarsu Kenya, a ranar 6 ga watan Fabrairun 1952 labarin mutuwar mahaifinta ya iso su, daga nan aka ayyana Elizabeth II ta zama sabuwar sarauniyar Ingila.
5. Alakarta da Najeriya
A tarihi, sarauniya Elizabeth II ce kadai sarauniyar da ta taba mulkar Najeriya, wacce hakan yasa ake kiranta da Sarauniyar Najeriya a hukumance.
An soke wannan sarautar ne a ranar 1 ga Oktoban 1963, lokacin da Najeriya ta karbi shugabancinta gadan-gadan.
Najeriya ta kasance a kasan kafafun sarauniya Elizabeth tun shekarar 1960 har zuwa 1963, lokacin da kasar ta karbi lamurranta gaba bayan samun 'yanci a 1960.
6. Ballewar annobar Korona
A shekarar 2020, annobar Korona ta barke a kasashen duniya, don haka Ingila ma bata tsira ba. Wannan yasa aka dauke sarauniyar daga masarautar dake Burtaniya zuwa gidan sarautar Windsor duk dai a kasar.
Bayan karfafawa mutanen kasarta gwiwa cewa, annobar Korona za ta wuce nan kusa, an ga sarauniyar a watan Janairun 2021 tana karbar allurar rigakafin Korona. Ta kuma sake yin allurar a watan Afrilun shekarar.
7. Rasuwar mijinta
A ranar 9 ga watan Afrilun 2021 ne aka shiga jimamin mutuwar mijin sarauniya Elizabeth, wato Yarima Phillip bayan shafe shekaru 73 a rayuwar aurensu.
Kasancewarta sarauniya mafi dadewa a tarihin masarautar Ingila, itace kuma ta biyu cikin jerin matan da suka hau karagar da suka rasa mazajensu; dayar itace kakarta sarauniya Victoria.
8. Bikin cika shekaru 70 a karagar mulki
A ranar 6 ga watan Fabrairun 2022 ne aka fara bukukuwa cikar sarauniya Elizabeth 70 a kan karagar mulkin Ingila.
A wannan watan dai aka dan samu tasgaro, sarauniyar ta kamu da annobar Korona, lamarin da yasa aka dage ci gaba da bikin, kamar yadda BBC News ta kawo.
A ranar 13 ga watan Yunin 2022, aka rattaba ta a matsayin sarauniyar da ta fi dadewa a kan karagar mulki.
9. Nada sabuwar firaimistan Burtaniya
A ranar 6 ga watan Satumban 2022, kwanaki biyu kafin rasuwarta ta tabbatar da nada Liz Truss a matsayin sabuwar firaiministan kasar Burtaniya.
Kafin wannan sabon nadi, an dan dauki lokaci ba a ga sarauniyar a bainar jama'a ba.
10. Rasuwarta
A yau kuma, 8 ga watan Satumba, sanarwa daga masarautar ta sanar da cewa ta dan tashi da rashin lafiya.
Bayan awanni kadan, aka sanar da rasuwar ta da yammacin yau Alhamis 8 ga watan Satumban bana.
Tuni aka nada dan Yarima Charles don ci gaba da rike sarautar.
Littafin tarihin masarautar Ingila na Gyles Brandreth ya kawo cikakken tarihin sarauniyar Ingila da ma sauran wadanda suka yi mulki a kasar.
Asali: Legit.ng