Bam Ya Fashe a Masallacin Herat Na Afghanistan, Fitaccen Limami Ya Rasu
- Yanzu muke samun labarin mutuwar wani fitaccen malamin addinin Islama a kasar Afghanistan
- Bam ya tashi a wani masallaci, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, gwamnatin kasar ta magantu
- Ana yawan samun hare-haren bama-bamai a Afghnanistan cikin kwanakin nan, IS ke daukar alhakin harin
Herat, Afghanistan - An samu fashewar bam a daya daga cikin manyan masallatan yammacin Afganistan a ranar Juma'a, inda aka rasa wani babban limami.
Limamin dai shi ne ya yi da'awar kashe duk wani da ya yi inkari da manufofin gwamnatin Taliban a farkon wannan shekara, rahoton The Guardian.
Hotunan da aka ta yadawa a Twitter sun nuna jini kaca-kaca a masallacin na Gazargah da ke birnin Herat. Kafofin yada labaran kasar shaida cewa, ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu.
An rage samun tashe-tashen hankula a Afghanistan tun bayan da kungiyar Taliban ta karbe mulki bara, sai dai akan yawan samun tashin bama-bamai a kasar cikin 'yan watannin nan. Kungiyar ta'addanci ta IS ce amsa kitsa dukkan hare-haren.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnatin Taliban ta yi magana
Kakakin gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid ya tabbatar da mutuwar Mujib ur Rahman Ansari a harin na ranar Juma'a.
A cewar Mujahid ta shafin Twitter:
"Bujumin malamin addini mai tsananin kwarjini na kasar nan ya yi shahada a wani mummunan hari."
Hakazalika, ya bayyana ta'aziyyarsa ga iyalai da dangin malamin da kasar ke matukar ji dashi ko koyarwarsa.
Ansari dai fitaccen malami ne mai fada a ji a Afghanistan, kuma ya shahara da fadin zafafan kalamai masu jawo cece-kuce.
An harbe mahalarta daurin aure a Afghanistan saboda sun saurari wake-wake
A wani labarin, akalla mutane biyu da suka halarci wani daurin aure a gabashin kasar Afghanistan aka kashe a ranar Juma’a, 29 ga watan Nuwamba, 2021.
CNN ta fitar da rahoto a makon nan, tace an kashe wadannan Bayin Allah ne saboda sun saurari waka.
Ana zargin wasu ‘yan kungiyar Taliban da wannan aika-aika, inda suka budawa masu halartar wannan biki wuta. Hakan ya yi sanadiyyar rasa Bayin Allah.
Asali: Legit.ng