Wani dan kasar Ukraine ya Musulunta bayan ya samu mafaka a masallaci
- Wani dan kasar Ukraine da yakin Rasha ya shafa ya karbi addinin Islama bayan samun mafaka a hannun Musulmi
- Voronko Urko ya bayyana kadan daga tarihinsa da kuma yadda yaki ya kai ga rugujewar iyalinsa da 'ya'yansa
- Limamin masallaci ya ba da labarin yadda suka hadu har ya samu mafaka a masallaci kana ya zama na gida
Ukraine - Wani dan gudun hijira daga Ukraine, Voronko Urko ya karbi addinin musulunci bayan samun gata daga musulmai a wani masallacin da ya samu mafaka.
Bayan da yaki ya barke tsakanin Rasha da Ukraine a farkon shekarar nan, rikicin ya kai ga rugza gidan Urko da ke birnin Kharkiv a Ukraine, lamarin da yasa ya yi gudun hijira, inji rahoton BBC.
Da yake ba da tarihinsa, ya ce kafin barkewar yakin yana zaune lafiya da matar da 'ya'yansa mata biyu, amma yanzu gidan nasa ya ruguje kuma iyalansa sun watse.
Yadda lamarin ya faru
A wani bidiyo da wakilinmu ya gani daga TRT World, inda Urko ke ba da labarin yadda ya tsira daga yakin, ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Lokacin da ’yan agaji suka dauke iyalina zuwa wani wuri a ranar 8 ga Maris, sun bar ni ni kadai. Nakan je mafakar daga hawa na 9 duk lokacin da aka kai hari. Babu iskar gas, babu ruwa."
Muhammad Ali, limamin masallacin da Urko ya samu mafaka ya ba da labarin yadda haduwarsu ta kasance da kuma yadda ya karbi addinin Islama.
A cewarsa:
"Sa'ad da lamarin ya kara kamari, sai ya kira ni ya ce 'Ali don Allah ka dauke ni'. Tun daga nan ya zauna a masallacinmu kuma muka zama ‘yan’uwa."
Kuyi hattara, zamu diro kanku kamar yadda mukewa Ukraine: Rasha ta gargadi Finland da Sweden
A wani labarin, gwamnatin kasar Rasha ta gargadi kasashen Finland da Sweden kan shirin shiga kungiyar NATO da sukeyi, tace ba zai amfanar da Turai da komai ba.
Dmitry Peskov, Mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, yace shiga NATO tamkar fito-na-fito ne da kasar Rasha, rahoton BBC.
Jami'an kasar Amurka sun ce kasashen dake makwabtaka da Rasha zasu fara shiga kungiyar NATO daga watar Yuni.
Asali: Legit.ng