Bidiyo: Cike da Alfahari, Budurwa Ta Bayyana Saurayinta Kafinta, Ta Rungumeshi Tare da Sumbatarsa

Bidiyo: Cike da Alfahari, Budurwa Ta Bayyana Saurayinta Kafinta, Ta Rungumeshi Tare da Sumbatarsa

  • Wata budurwa 'yar Najeriya ta bayyana wata irin soyayya da take wa saurayinta wanda sana'arsa kafinta ce, kuma ta bar mutane baki bude
  • Budurwar ta bayyana saurayinta kafinta cike da alfahari yayin da ta bukaci ya rungume ta yayin da yake tsaka da aikin neman halas dinsa
  • Bayan ya rungumo budurwa, ta kara da sumbatarsa, lamarin da yasa jama'a suka dinga yaba mata kan yadda take kaunarsa da alfahari da aikinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani bidiyon budurwa 'yar Najeriya tana bayyana saurayinta cike da alfahari ya birge jama'a. Ba saurayin ne da soyayyar bace kadai abun birgewa, har da yadda ta bayyana sana'arsa ta kafinta ba tare da ta kyamacesa ko raina shi ba.

Masoyan Juna
Bidiyo: Cike da Alfahari, Budurwa Ta Bayyana Saurayinta Kafinta, Ta Rungumeshi Tare da Sumbatarsa. Hoto daga TikTok/@morningmoon44
Asali: UGC

A bidiyon da ta wallafa a TikTok, budurwar ta nadi saurayinta yana tsaka da aiki kuma ta sanar da shi cewa tana bukatar ya rungumeta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: 'Saurayina Ya Koma Turai Da Zama Mako 1 Bayan Ya Nemi Aurena', Labarin Wata Budurwa Mai Tsima Zuciya

Duk da aikin da yake yi, ya nuna mata hanyar da zata bi ta zo kusa da shi ba tare da ta samu rauni ba. Tana isa wurin da yake, budurwar ta rungume shi tare da sumbatarsa.

Ta kara da shawartarsa cike da kulawa cewa ya kiyaye da kusoshi sannan suka dauka bidiyon kansu yayin da suke cikin shaukin kauna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalla bidiyon a kasa:

Bidiyon Kyakyawar Baturiya da Gudu Tana bin Matashi Bakar Fata don ta Karba Lambarsa

A wani labari na daban, wani matashi bakar fata ya hadu da wata kyakyawar budurwa baturiya kuma ya yanke hukuncin taya ta a karon farko cike da dabara da kwarewa a soyayya.

Ya tunkari budurwar ta bayanta inda ya taba ta a kafada tare da bata kyautar kyakyawar balan-balan.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Yayin da Ta Iso Najeriya Don Haduwa Da Saurayinta Na Soshiyal Midiya

Kyakyawar budurwar ta karba ba tare da bata lokaci ba, amma ba a hakan aka tsaya ba. Matashin ya durkusa da guiwarsa a kasa tare da sumbatar hannunta yayin da ta mika masa babu jinkiri a cikin jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel