Shahararrun Kasashe 5 Da Mata Ke Auren Mazaje Fiye Da Daya a Lokaci Guda

Shahararrun Kasashe 5 Da Mata Ke Auren Mazaje Fiye Da Daya a Lokaci Guda

Yayin da mafi yawancin kasashe sun hallasta wa maza auren mata daya ko fiye da hakan, kasashe kadan ne suke yarda mata su auri maza fiye da daya, abin da ake kira 'Polyandry'.

Ba sabon abu bane namiji ya auri mata fiye da daya, addinai da al'adu da dama sun hallasta hakan.

Maza da matarsu.
Kasashe 5 Da Mata Ke Auren Mazaje Fiye Da Daya a Lokaci Guda. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

Amma, ba kasafai ake ganin yanayi da mace ke auren maza fiye da daya ba a lokaci guda, amma akwai wasu kasashe da hakan ke faruwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wannan rubutun, kamar yadda The Nation ta rahoto, ga jerin kasashen da mata ke auren maza fiye da daya a lokaci guda;

1. Indiya

Al'ummar Paharis na yankin Jaunsarbawar na yankin arewacin Indiya da wasu tsirarun mutanen Kinnaur, Himachal suna auren maza fiye da daya a lokaci guda.

Kara karanta wannan

'Yan PDP Sun Shiga Zulumi, An yi Taron Gangamin Kamfen, Fili a Bushe a Wata Jahar Arewa

A matsayinsu da mutanen da suka fito daga tsatson Pachi Pandavas (wata yan uwa biyar da suka aure mata daya mai suna Draupadi, yar sarki Panchala), sun yi imanin cewa ya kamata su cigaba da al'adar.

Mutanen kabilar Nilgiris, Najanad Vellala na Travancore da wasu yan Nair a kudancin Indiya.

A 1988, Jami'ar Tibet ta yi bincike kan iyalai 753 a Tibet ta kuma gano kashe 13 cikin 100 suna al'adar Polyandry.

2. Kenya

Yayin da gwamnatin Kenya bata haramta Polyandry ba karara, ana aikata hakan a fili. An fara rahoto auren Polyandry ne a shekarar 2013 a Kenya a lokacin da wasu maza biyu suka auri wata mace guda da suke so.

Amaryar ta gaza zaben daya cikinsu, hakan ya bata daman auren dukkansu. An samu rahotannin Polyandry a al'ummar Massai na Kenya.

A shekarar 2013, wasu maza yan Kenya su biyu sun auri wata mace da suke soyayya da ita.

Kara karanta wannan

Kamar almara: Wani ya hango nasarar Morocco kan Portugal, 'yan Najeriya sun yi caca a kai, sun ci miliyoyi

3. China

A kasar China na yanzu, mutanen da ke zaune a yankin Tibet da wasu kabilu kamar Monpa, Tamang, Qiang, Sherpa da Lhoba, kuma akwai mutanen Han Chinese da Hui a yankin.

A zamanin da, mutanen yankunan suna auren maza da yawa. Matar bata bayyana ko wanene mahaifin yaranta domin kada a samu rashin jituwa tsakaninsu.

Amma, gwamnatin Tibet a 1981 ta yi dokar hana auren maza fiye da daya.

Duk da dokar, bincike ya nuna har yanzu wasu mutane ba su dena ba.

A halin yanzu, ana Polyandry a yankunan Tibet, musamman a karkara na Tsang da Kham inda ake fama da talauci.

Wani bincike da aka yi a 2008 a kauyukan Xigaze da Qamdo ya nuna kashi 20-50 na iyalan suna auren maza fiye da daya, mafi yawancinsu maza biyu suke aure. A kauyuka, adadin ya kai kashi 90 cikin 100.

Ba a cika samun Polyandry ba a birane.

Kara karanta wannan

Iyalai A Nigeria Na Hakura Da Ci Su Koshi Sabida Yanayin Tashin abinci

4. Nepal

Nepal kasa ce da ke Kudancin Asia a yankin tsaunikan Himalayas.

Gwamnati ta hana auren maza fiye da daya a Nepal tun 1963, amma mutane a Humla, Dolpa, da Kosi har yanzu suna cigaba da wannan al'adar.

Akwai wasu kauyuka da baki dayansu wannan al'adar suke yi.

An fi samun wannan auren ne tsakanin mutanen Kudancin Nepal da arewa maso gabas, ciki har da Bhote, Sherpa, Newbie da wasu wurare.

5. Gabon

Maza da mata suna iya auren abokan zama fiye da daya karkashin dokar Gabon. A aikace maza ne kawai ke auren mata fiye da daya.

A watan Mayun 2021, wata mata yar Gabon ta nuna mazajenta guda bakwai ta kuma yi bayanin yadda ta ke zaune da su ba tare da samun matsala ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164