An yi wa amarya da angon da suka rasu shekaru 30 da suka wuce bikin kece-raini a Indiya

An yi wa amarya da angon da suka rasu shekaru 30 da suka wuce bikin kece-raini a Indiya

  • An daura auren wasu matattun amarya da ango da suka rasa rayukansu shekaru 30 da suka gabata a wani bikin kece-raini a Indiya
  • Kamar yadda Anny yayi bayani, yaran da suka rasu suna kanana a kan hada su aure bayan sun kai shekarun girma a mace
  • Ya bayyana cewa, sau da yawa iyayen jariran da suka rasu kan bazama nemawa matattun 'ya'yansu abokan rayuwa, sai a yi auren idan sun girma

Wata amarya da angonta da suka rasa rayukansu shekaru 30 da suka gabata sun yi aure a wani gagarumin bikin kece-raini wanda ya samu halartar 'yan uwansu da abokan arziki a Indiya.

Wani ma'abocin amfani da Twitter 'dan kasar Indiya mai suna @anny_arun ne ya bada labarin yadda auren ya kasance.

Ya yi bayanin cewa, a al'adarsu idan mutum ya mutu yana karami, iyalan mamacin na iya nemo wani wanda ya rasu yana karami ta yadda za a yi musu aure.

Kara karanta wannan

Yadda Bidiyon Kyawawan Angwaye Ya Kirkita Mata A Soshiyal Midiya, Wata Tace Angon Take So

Dead bride and groom
An yi wa amarya da angon da suka rasu shekaru 30 da suka wuce bikin kece-raini a Indiya. Hoto daga indiatoday.in
Asali: UGC

Ya kara da cewa, hakan ake yi wa jinjirai da suka mutu yayin haihuwa. Iyayen jariran mace da namiji sai su amince kuma su aurawa 'ya'yansu matattun juna idan sun girma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace duk da wadannan mutanen sun rasu, ba wasa bane nemo musu aure a gari saboda iyayen wani mamacin na iya hana bada auren nasa mamacin.

Yace iyayen wani mataccen yaro sun hana aurensa ga wata matacciyar yarinya saboda sun ce an haifeta kafin shi hakan yasa ya girmeta.

A bidiyoyin bikin auren matattun, an ga iyayen ma'auratan suna ta shagali tare da bikin a madadin mamatan.

An shirya kujeru wadanda ake warewa mamatan ma'auratan tare da kayayyakin amarya da angon da aka saka a kan juna.

Yadda budurwa ta shiga bariki, bayan shekaru 6 ta koma gida da cutukan kanjamau da TB

A wani labari na daban, wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai amfani da sunan @soltune ya bayyana yadda 'yar uwar shi ta bar gida, bayan shekaru shida kuma ta dawo musu da cutukan Kanjamau da TB wanda daga bisani ta warke.

Kara karanta wannan

Cike da tashin hankali, matashi ya sanar da mutuwar budurwar da zai aura nan da sati 2

Kamar yadda Soltune yace, 'yar uwarshi ta bar gida a shekaru shida kuma bata dawo ba har sai shekarar da ta gabata yayin da wasu mutane suka kawo ta gida magashiyyan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng