Bidiyon doguwar budurwa mai shekaru 22, tana da tsayin ban mamaki
- Wata budurwa ta birge jama'a da yawa da tsayinta yayin da take takun kasaita a cikin jama'a kuma take daukar hankali
- Jama'a da suka ga yadda ta wuce su a tsayi sun dinga daga kai suna kallon ta a lokacin da take takawa tana wuce su
- Ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamani ta TikTok sun cika sashin tsokaci kan yadda tsayin yayi mata kyau matuka
Wata matashiyar budurwa ta bayyana irin tsayinta a wani bidiyon TikTok da ta fitar.
A farkon bidiyon, ta zauna inda ta tallabe kuncinta a hannunta. Kalaman da aka rubuta a kasan bidiyon sune: "Idan ka cigaba da girma har ka kai shekaru 22 duk da ke yarinya mace ce."
Kowa na gajarcewa idan ya tsaya a gefenta
Ta tashi tsaye ta tattaka a cikin jama'a
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk wanda ya tsaya a gefenta sai ya zama gajere koda kuwa tsayinsu daidai yake. Akwai wasu masu wucewa da suka kasa hakuri har sai da suka dinga kallonta.
Ba tare da ta damu da yadda ake kallonta, ta cigaba da tafiya. Ga bidiyon budurwar:
Jama'a sun yi martani
A yayin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya samu yabo 100,000 tare da dubban tsokaci.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin.
Moestuinieren me Ronald yace: "Ki ziyarci arewacin Netherlands, sai kin koma mai matsakaicin tsayi."
Ta yi masa martani da: "Ina tantamar hakan."
Memzul786 yace: "Wata kawata tana ta tsawo a France, likitoci sun saka ta kan wasu magunguna."
Sire_Adel yace: "Abinda zan yi shine auren yarinya mai tsayinki. Kina da tsananin kyau."
Emma Walherim yace: "Nima haka na dinga tsayi har na kai shekaru 25."
Karuwa Ta Sharbe Farjin Takwararta Da Reza Bayan Fada Ya Kaure Tsakaninsu Kan Kwastoma, Ta Shiga Hannu
Yadda budurwa ta shiga bariki, bayan shekaru 6 ta koma gida da cutukan kanjamau da TB
A wani labai na daban, wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai amfani da sunan @soltune ya bayyana yadda 'yar uwar shi ta bar gida, bayan shekaru shida kuma ta dawo musu da cutukan Kanjamau da TB wanda daga bisani ta warke.
Kamar yadda Soltune yace, 'yar uwarshi ta bar gida a shekaru shida kuma bata dawo ba har sai shekarar da ta gabata yayin da wasu mutane suka kawo ta gida magashiyyan.
Asali: Legit.ng