Bidiyo: Da kudin budurwa ta tafi dakin saurayi, ya toshe kiran ta yayin da take hanyar zuwa
- Wata budurwa ta bayyana fushinta bayan saurayin da suka hadu a Tinder ya karta mata wulakancin da ba zata manta ba
- Bayan haduwarsu da kwanaki, ta kwashi kafa daga garinsu don kai masa ziyara har gidansa amma ya toshe kiranta daga shiga wayarsa
- Budurwa ta bayyana yadda tayi kudin motarta da kanta, hakan yasa ta rasa inda za ta yi ko kuma ina zata je bayan ya toshe ta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Wata budurwa 'yar kasar Afrika ta kudu ta bada labarin abinda ta fuskanta yayin da ta kama hanyar zuwa kai wa saurayin da suka hadu a dandalin sada zumuntar zamani ziyara.
Tace wannan ne karo na farko da suka hadu a wata manhajar hada samari da 'yan mata mai suna Tinder kuma ta yanke hukuncin kai masa ziyara a wani gari.
Budurwa ta amince zata kwanta da saurayi, ta roke shi N15k, ya danna mata ashar tare da cewa ziciyarta ta mutu
Budurwar ta wanke kafa inda ta hau mota tun daga garinsu mai suna Limpopo, ta tafi Durban da fatan haduwa da matashin da suka fara soyayya.
A bidiyon da ta wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, ta yi ikirarin cewa ya toshe ta kuma ta kara kiransa yayin da take mota bayan sun dade da tasowa daga Limpopo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lamarin ya fusata budurwar saboda tayi amfani da kudinta wurin biyan kudin mota amma ya saka ta a mawuyacin hali don bata san abinda za ta yi ba ko inda zata je.
Yadda budurwa ta shiga bariki, bayan shekaru 6 ta koma gida da cutukan kanjamau da TB
A wani labari na daban, wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai amfani da sunan @soltune ya bayyana yadda 'yar uwar shi ta bar gida, bayan shekaru shida kuma ta dawo musu da cutukan Kanjamau da TB wanda daga bisani ta warke.
Kamar yadda Soltune yace, 'yar uwarshi ta bar gida a shekaru shida kuma bata dawo ba har sai shekarar da ta gabata yayin da wasu mutane suka kawo ta gida magashiyyan.
Ya wallafa hotunan kanwar shi a lokacin da wasu suka kawo ta gida da kuma lokacin da ta warware kamar ba ita ba a ranar 27 ga watan Yulin 2022.
"A wannan shaidar, kai tsaye zan je kan maganar abinda zan tattauna a kai, babu dogon labari. Shekaru shida da suka wuce, 'yar uwata ta tashi ta bar gida haka kawai. A cikin wadannan shekarun, na rasa mahaifina da 'yar uwata, mahaifiyata da 'yan uwana suna shan wahala amma mun cigaba da addu'a da yarda da Ubangiji," yace.
Asali: Legit.ng