"Gumi Na Ne", Faston Da Aka Yi Wa Fashin Gwala-Gwalai Yayin Da Ya Ke Wa'azi A Mimbari A Coci Ya Magantu

"Gumi Na Ne", Faston Da Aka Yi Wa Fashin Gwala-Gwalai Yayin Da Ya Ke Wa'azi A Mimbari A Coci Ya Magantu

  • Bishop Lamor Miller-Whitehead, wani babban fasto da ke Brooklyn a kasar Amurka da aka yi wa fashi a cikin cocinsa ya magantu
  • Bishop Miller-Whitehead ya ce ba laifinsa bane fashin da aka masa kamar yadda wasu ke cewa wai saboda ya cika nuna arzikinsa a fili ne
  • Malamin addinin kiristan ya ce yana da damar kashe kudinsa ya siyo duk abin da ya ke so saboda dama guminsa ne ba na wani ba

Limamin coci 'dan kwalisa' na jihar Brooklyn wanda ya saba nuna kayayyakinsa masu tsada ya kare kansa bisa rayuwa ta tunkaho da ya ke yi bayan an masa fashi yana tsakar wa'azi, rahoton Lindaikeji.

Bishop Lamor Miller-Whitehead wanda ke kan mimbari lokacin da wasu mutane suka shigo cocin suka sace masa kayan allatu tare da na matarsa da kudinsu ya kai $1m.

Kara karanta wannan

Bana karbar canji, manyan kudi nake so: Bidiyon 'dan sanda mai karbar cin hanci babu tsoro

Bishop Whitehead.
"Gumi Na Ne" Faston Da Aka Yi Wa Fashi Yayin Da Ya Ke Wa'azi A Coci Ya Magantu. @lindaikeji.
Asali: Twitter

Miller-Whitehead wanda ya yi fice wurin salla tufafi masu tsada na Gucci, da sarkoki masu tsada da motocci, ya yi wannan martanin ne bayan wasu mutane sun ce laifinsa fashin da aka masa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yanzu ya ce ba laifinsa bane fashin da aka masa.

Bishop Lamor Miller-Whitehead, wanda a baya an taba tura shi gidan gyaran hali saboda damfara, ya dage kan cewa nuna arzikinsa a Instagram ba shine dalilin da yasa aka yi masa fashin ba a Canarsie.

Ina da damar siyan duk abin da na ke so, Bishop Miller-Whitehead

Malamin addinin mai shekaru 44 ya ce: "Ba batun nuna arzikina bane. Magana ne na siyan abin da na ke son in siya. Ina da damar siyan duk abin da rai na ke so."

Bishop din ya ce ba zai yi wu a dora masa laifi saboda yana da arziki a garinsu.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ɗan dambe ya lakaɗi matashin da ya zungure shi a Twitter kuma ya bi shi har gida su goge raini

Ya kara da cewa: "Wasu lokutan idan an san ka a matsayin Bishop, baiwa ce kuma matsala ne. Duk za a saka maka ido a gari."

A lokacin da aka masa fashin, Miller-Whitehead da matarsa suna sanye da kayan alatu na gwal na $1m.

Barayin sun sace masa kaya da kudinsu ya kai $1,060,000: Agogon Rolex na $75,000, Agogon Cavalier ta $75,000, zobe ta diamond da ruby $25,000, zoben Episcopal na zinari na $25,000, yan kunne na $25,000, kuros na zinari da emerald na $20,000, zoben Episcopal na $20,000, kross na Episcopal da kuros ta $10,000 na gwal ta $20,000.

Dirama yayin da 'yan fashi suka dura coci ana tsaka da bautar ranar Lahadi, suka yiwa fasto da mabiyansa fashi

Tunda farko, kun ji cewa an yi wa wani babban fasto na Brooklyn fashi a lokacin hidimar bauta da aka yi ta kai tsaye a ranar Lahadi, 24 ga Yuli.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

Kamar yadda aka gani a cikin wani faifan bidiyo, faston ya ga shigowar wasu tsageru rike da bindiga cocinsa a lokacin da yake kan mimbari yana kwada wa'azin ranar Lahadi.

Jaridar New York Post ta ruwaito cewa tsagerun sun tafi da kayan ado na karafa masu daraja da suka kai KSh miliyan 47, a cewar masu bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164