Karyewar Crypto: Shugaban Binance da wasu attajiran Crypto 10 da ke ganin karayar arziki
- A cikin watanni takwas da suka gabata, biliyaniyoyin crypto sun ga durkushewar dukiya cikin sauri kamar dai yadda kudin suke mara tabbas
- A zahiri, tsakanin 1 ga Janairun 2022 zuwa Laraba, 13 ga Yuli, biliyanoyin crypto bakwai sun ga tasgaro a yawan dukiyarsu na sama da dala biliyan 100 a jumillance
- Duk da yake suna da kyakkyawan fata game da sake dawowa da karfinsu, kasuwar na kara dagulewa, hakan na kuma nuna cewa karin asara na nan tafe
Wadannan ba lokata ne masu kyau ga 'yan crypto ba, haka kuma ga wadanda suka dafshi romon dukiya mai yawa daga gare ta.
A cikin 'yan shekaru kadan, masana fasaha masu tasowa sun zama mazaje abin kwatance a duniya bayan da suka tara biliyoyin daloli daga sayar da kadarorin su na zamani ta yanar gizo.
A cikin jerin masu arziki na Forbes na 2022, 19 daga cikin sunayen da aka kawo duk sun sami kudinsu ne daga harkallar crypto.
Manya a jerin su ne Changpeng Zhao, Sam Bankman-Fried, da Brian Armstrong - duk kuma sanannu ne a duniyar crypto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar rahoton Bloomberg, ’yan crypto bakwai sun tara darajar dalar Amurka biliyan 145 a ranar 9 ga Nuwamban bara, lokacin da Bitcoin ya kai kusan dala 69,000.
Cikin watanni shida bayan haka, dukiyar mutanen bakwai da suka mori kasuwar crypto, sun yi asarar dala biliyan 114 a jumillance.
Misali, mutumin da ya fi kowa arzikin crypto Changpeng Zhao, wanda ya kafa Binance, a ranar 31 ga Maris 2022, ya mallaki akalla dala biliyan 64.5 kuma na 19 a jerin attajiran duniya.
A ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, darajarsa ta ragu zuwa dala biliyan 19, kuma ya fadi zuwa na 76.
Jerin attahiran crypto 10 a jadawalin Forbes
Ga dai jerin attajiran na crypto da dukiyar da suka mallaka:
Suna | Tushen Arziki | Kiddigar dukiya daga Forbes |
Changpeng Zhao | Binance | $65bn |
Sam Bankman-Fried | FTX | $24bn |
Brian Armstrong | Coinbase | $6.6bn |
Chris Larsen | Ripple | $4.3bn |
Cameron Winklevoss and Tyler Winklevoss | Bitcoin | $4bn kowannensu |
Song Chi-Hyung | Upbit | $3.7bn |
Barry Silbert | Digital Currency Group | $3.2bn |
Jed McCaleb | Ripple, Stellar | $2.5bn |
Nikil Viswanathan and Joseph Lau | Alchemy | $2.4bn kowannensu |
Devin Finzer and Alex Atallah | OpenSea | $2.2bn |
Ci gaba: Dangote ya sake banke mutum 20, ya zama na 63 a jerin masu kudin duniya
A wani labarin, attajirin Najeriya Aliko Dangote ya zama na 63 a jerin attajirai a duniya, kamar yadda wani sabon jadawali na Bloomberg ya nuna.
A cikin kididdigar da aka fitar jiya, shugaban Tesla, Elon Musk, ya fito a matsayin attajirin da ya fi kowa kudi a duniya har ila yau, rahoton Vanguard.
Dangote, wanda ya haura matsayi 37 a jerin attajiran Bloomberg na baya-bayan nan, ya tara dala biliyan 20.2 ya zuwa ranar Litinin, 13 ga Yuli, 2022.
Asali: Legit.ng