Bidiyo: Yadda me kula da jakunkuna matafiya ya sace jirgin sama, yayi shawagi a sama, ya tafka hatsari
- Filin jiagen sama na Seattle sun saki bidiyon yadda mai kula da jakunkunan matafiya ya saci jirgin saman Alaska Airlines tare da lulawa sararin samaniya
- A bidiyon an ga yadda Russell ya shiga har ma'adanar jiragen saman tare da fito da jirgin inda ya tuka shi ya dinga shawagi kafin ya tafka hatsari a wani tsibiri
- Russell ya kwashe sa'a daya da minti 13 ana rokonsa tae da masa magiya kan ya sauko kasa, amma ya dinga zolayar masu kula da jiragen da yake magan dasu
Wani sabon bidiyo ya nuna lokacin da mai kula da jakunkunan matafiya a filin jirgin sama ya sace jirgin sama na kamfanin Alaska Airlines kafin daga bisani ya tafka hatsari da gangan a wani tsibiri inda ya rasa ransa.
Hukumomin a filin jirgin sun saki bidiyon CCTV daga kamarorinsu na ciki da wajen filin wanda ya nadi yadda lamarin ya faru.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A bidiyon, matashin Richard Russell mai shekaru 29 yana aiki a filin jirgin saman matsayin mai kula da jakunkunan matafiya. An gan shi ya ratsa ta wurin jami'an tsaron filin jirgin sanye da riga mai gajeren hannu.
Bayan sa'o'i biyar, an ga Russell yana shiga wurin daake adana jirage kuma ya dauka jirgi tare da kama hanyar fita dashi.
Masu kula da tafiyar jiragen sama sun fara gane cewa akwai abunda ke faruwa kuma sun yi kokarin yin magana da wanda ke cikin jirgin amma basu samu martani ba.
An ga abokan aikin Russell suna kai kawo a wurin, basu san ya kusa shiga wurin tukin jirgin ba.
An ga Russell ya bude wurin matujan jirgin kuma ya shige mazaunin tare da tuka jirgin ya tashi sama.
"Mai kula da jiragen sama na Seattle. Na kusa tashi sama. Lallai akwai shagali yau," ya bayyana ga wadanda ke kula da jiragen.
Bidiyon da aka nada daga kasa ya bayyana yadda yake tafiyar ganganci da jirgin.
"Kai, gani a cikin wani hali. Ina sararin samaniya yanzu haka. Zan ta yawo ne kawai," aka ji shi yana fadi ta rediyon jirgin.
A sautikan muryoyin da aka nada, an ji yadda masu kula da jirgin ke ta kokarin shawo kanshi don ya sauka lafiya kalau.
Ana jin yadda Russell ya dinga zolayarsu.
A wani lokaci ma, ya tambaya daya daga cikinsu cewa: "Kai kana ganin idan na sauka lafiya Alaska zata bani aikin yi a matsayin matukin jirgin sama?"
Mai kula da jirgin yayi masa martani da "ka san, ina tunanin zasu iya baka kowanne irin aiki idan ka sauko lafiya."
Russell yayi martani da: "Eh gaskiya. A'a, ni bature ne."
An ji yadda suka dinga rokon Russell da ya sauka kuma suka dinga bashi umarni kan yadda hanyar take da yadda zai sauka.
"Akwai wurin sauka nan kusa da kai ta bangaren dama kusan mil daya ne tsakanin ku, ka ganshi?" Mai kula da jirgin yace.
"A'a wadannan zasu yi kokarin hukunta ni idan na sauka a nan...," Russell yayi martani. Kuma ina tunanin zan iya bata wani abu a wurin. Ba zan so yin haka ba. Ko kuma suna da abun harbo jiragen sama."
"Basu da shi, muna dai kokarin samo maka inda zaka sauka lafiya ne," mai kula da jirgin yayi martani.
Russell ya sanar da shi cewa bai shirya sauko da jirgin saman ba.
"Sai dai amma ya dace in dena kallon wurin mai, saboda yana karewa da gaggawa," ya kara da cewa.
"Toh Rich, idan zaka iya, zaka iya juyawa hagu mu kai ka kudu maso gabas ka sauka." Mai kula da jirgin yace.
"Iyyeh, ina tunanin zaman gidan yari zan yi har abada," Russell yace.
An yi yunkurn ceo Russell
Jiragen yaki biyu sun tashi daga Portland mintoci kadan bayan tashin jirgin saman domin su tare shi.
Sai dai basu samu nasara ba, bayan sa'a daya da mintoci 13, Russell ya kifar da jirgin saman da gangan a wani tsibiri, lamarin da yayi ajalinsa.
FBI sun yanke hukuncin cewa, kashe kansa yayi kuma sun ce lamarin bashi da wata alaka da mummunan laifi ko ta'addanci tunda Russell shi kadai ya shiga jirgin.
Asali: Legit.ng