Gudun layya yake? Bidiyon rago ɗare-dare a rufin bene mai hawa 2 ya nishaɗantar da jama'a

Gudun layya yake? Bidiyon rago ɗare-dare a rufin bene mai hawa 2 ya nishaɗantar da jama'a

  • Wani bidiyo dake ta yawo a shafukan sada zumuntar zamani ya bayyana wani kosasshen rago a saman rufin bene mai hawa biyu
  • Bidiyon mai bada dariya na dabbar an gano cewa an dauke shi ne a Ajegunle dake jihar Legas inda mutane suka taru suna kallon ikon Allah
  • Masu amfani da kafar sada zumuntar zamani sun dinga tambayar yadda dabbar ta hau saman, amma wasu sun ce ragon gudun layya yake

Wani bidiyo ya bayyana inda wani rago ya haye rufin wani bene mai hawa biyu a Ajegunle dake jihar Legas, wanda yasa aka dinga tambayoyi kan yadda ragon ya kai nan.

A bidiyon da aka nada, dabbar ta dinga yawo a saman rufin gidan tana neman hanyar tserewa ko kuma sauka.

Kara karanta wannan

Sokoto: Kwastoma ya sharɓawa karuwa wuƙa bayan ta ƙi karbar N1,000 na 'aikinta'

Rago a bene
Gudun layya yake? Bidiyon rago ɗare-dare a rufin bene mai hawa 2 ya nishaɗantar da jama'a. Hoto daga @gboyegaakosile
Asali: Twitter

Har yanzu dai babu wanda ya san yadda ragon ya hau saman ginin.

An gano cewa an nadi bidiyon ne a yankin Ajegunle a jihar Legas, amma ba a san mamallakin ragon ba har a lokacin rubuta wannan rahoton.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yayin yada bidiyon mai bada dariya a Twitter, 'dan jaridan Najeriya mai suna Gboyega Akosile ya nemi taimakon mutane wurin sauko da ragon.

Ya rubuta: "Waye zai taimaka mana mu kama ragon nan dake yunkurin tserewa."

Ga bidiyon:

Jama'a sun yi martani

@racheal_smile tace: "Ragon ya kai su inda ba su sani ba."
@zuezilmoney yace: "Karya ne, mutum ne ya kai shi saman nan. Ta yaya idan ba tsafi bane."
@wrldprincecharming yayi martani da: "Tambayar kamata yayi ta kasance, ta yaya ragon ya kai nan."
@mr_landlordd yace: "Bai kamata a ci naman irin wannan ragon ba, akwai dalili."

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Budurwa ta haifo yaro ba tare da kwanciya da namiji ba, ta yi bayani dalla-dalla

A wani labari na daban, wata mata mai suna Aba tayi ikirarin cewa ta dauka ciki kuma ta haihu ba tare da ta sadu da namiji ba.

Yayin zantawa da Barima Kaakyire Agyemang a step 1 TV, Aba tayi ikirarin cewa shekara hudu rabonta da kwanciya da namiji.

Kamar yadda tace, lokacin da ta fara fuskantar wani irin ciwon ciki da kumburi, tace tayi tunanin cutar fibroid ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng