Da Dumi-Ɗumi: An ga jinjirin watan Babbar Sallah a Saudiyya

Da Dumi-Ɗumi: An ga jinjirin watan Babbar Sallah a Saudiyya

  • Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan babbar Sallah wato Dhul-Hijjah na shekarar 1443/2022 ranar Laraba
  • A wata sanarwa da Haramain Sharifai ya fitar, ta ce gobe Alhamis, 30 ga watan Yuni, 2022 zai kama ɗaya ga wata
  • Hakan na nufin maniyyata Hajjin bana zasu yi hawan Arfa ranar Jumu'a, yayin da za'a yi babbar Sallah ranar Asabar 9 ga Yuni

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa an ga jinjirin watan Dhul-Hijjah, watan babban Sallah yau Laraba 29 ga watan Dhul-Qa'adah 1443. Hakan na nufin ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, zai zama ɗaya ga wata.

Ganin watan na nuni da cewa al'ummar Musulmi a Saudiyya zasu gudanar da babbar Sallah (Eid-El-Adha) ranar Asabar 9 ga watan Yuni, 2022dai-dai da 10ga watan Dhul-Hijjah 1443.

Yadda ake duban wata a Saudiyya.
Da Dumi-Ɗumi: An ga jinjirin watan Babbar Sallah a Saudiyya Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shafin da ke kula da manyan masallatai biyu masu tsarki Haramain Sharifai, ya fitar a Facebook.

Kara karanta wannan

Tallafin fetur: Majalisa za ta binciki Gwamnatin Buhari, ta ce an sace Naira Tiriliyan 2.9

Snaarwan ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An ga jinjirin watan Dhul Hijjah 1443 a Saudiyya, saboda haka gobe Alhamis 30 ga watan Yuni, 2022 zai kama ɗaya ga wata, kafin Majalisar koli ta sanar a hukumance."

Watan Dhul-Hijjah shi ne wata na 12 a jerin watannin da ke Kalandar Musulunci kuma wata ne da al'ummar Musulmin duniya ke gudanar da Sallah yanka a cikinsa.

A wannan wata neaniyya ke aikinsu Hajji, wanda ɗaya ne daga cikin ginshiƙan addinin Musulunci guda biyar ga wanda Allah ya ba iko.

Haka zalika a wannan wata ne maniyyata ke hawa Arfa, ranar 9 ga watan Dhul-Hijjah, wato ranar Jumu'a 8 ga watan Yuni, 2022.

Kwanakin 10 na farkon wannan wata, wani lokaci ne da fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW) ya kwaɗaitar da Musulmai su ribace su da kyawawan ayƴuka, kama daga Azumi, Sadaka, ambaton Allah da sauran su.

Kara karanta wannan

Babban Sallah: Majalisar Dattawan Najeriya Ta Tafi Hutu, Ta Sanar Da Ranar Dawowa

A wani labarin kuma Wata maniyyaciya yar Najeriya daga jihar Nasarawa, Hajiya Aisha Ahmad, ta rasu a ƙasa mai tsarki

Hajiya Aisha Ahmed ta rasu ne a Asibitin Sarki Abdul'aziz kuma tuni aka gudanar da Jana'izarta kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Nasarawa ya ce marigayyar bata da rahoton rashin lafiya kafin tafiya Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262