Ka kawo mana jikoki ko ka bamu N270: Iyaye sun maka dansu a kotu bisa kin haihuwa
- Wasu ma’aurata sun maka dansu a gaban kotu saboda shi da matarsa sun ki haifa masu dan jikalle
- Ma’auratan wadanda yan asalin kasar Indiya ne, sunce dan nasu ya yi aure tsawon shekaru shida amma har yanzu baya tunanin haihuwa tare da matarsa
- Rokon da suke yi a kotu shine cewa imma dan ya biya su $650,000 (N270m) a matsayin diyya ko kuma ya haifa masu jika cikin shekara daya
Indiya - Wasu ma’aurata yan kasar Indiya masu suna Sanjeev da Sadhana Prasad sun maka dansu a kotu kan kin haifa masu jika, duk da ya shafe tsawon shekaru 6 da aure.
Ma’auratan wadanda ke cike da bakin ciki suna so ya saka masu domin sun kashe abun da suka tara a wajen tarbiyantar da shi da kuma basa ilimi.
Ma’auratan sun ba dan nasu zabi biyu
A karar da suka shigar a makon da ya gabata, The Times Indiya ta rahoto a ranar Alhamis cewa ma’auratan sun bukaci dansu da gimbiyarsa su biya $650,000 wato N270m ko su haifa masu jika cikin shekara daya.
“Danmu ya yi aure tsawon shekaru shida amma har yanzu basa tunanin haihuwa. Akalla idan muna da jikan da za mu dunga zama tare, radadin da ke ranmu zai ragu,” cewar ma’auratan a karar da suka shigar kotu a Haridwar, Indiya."
Ga rabe-raben kudin da Sanjeev da Sadhana Prasad suke so a biya su
Daily Star ta rahoto cewa ma’auratan da suka dauki bashi don gina gidansu suna fuskantar kalubale don haka suke so a basu toshiyar baki.
Suna so ya biya $80,000 (miliyan N33.2) da suka yi amfani da shi wajen siyawa dan nasu da matarsa motar alfarma.
Suna kuma so a biya su kudin da suka kashe wajen tura dan nasu cin angwanci a kasar waje da kuma na shagalin biki da aka yi a katafaren otel.
Iyayen sun kashe $65, 000 (miliyan N27) wajen horar da dan a matsayin matukin jirgin sama a kasar Turai, Gulf News ta rahoto. Sai dai ya dawo kasarsa Indiya ba tare da aiki ba.
A cewar lauyan ma’auratan Arvind Kumar, kotu za ta saurari karar da suka shigar a arewacin Indiya a ranar 17 ga watan Mayu.
Wata Mata Ta Jefi Ma'aikatan Lantarki Da Duwatsu, Ta Kuma Lalata Musu Lada Yayin Da Suka Zo Yanke Mata Wuta
A wani labari na daban, an gurfanar da Minotu Shodimu, mai shekaru 39 gaban kotun majistaren Ebute Meta da ke Jihar Legas bisa zarginta da lalata tsanin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarkin Eko (EKEDC).
Jaridar Vanguard ta ce wacce ake karar, tireda ce da ke zama a gida mai lamba 58 a titin Abule-Nla kusa da titin Apapa a Ebute Meta, kuma an gurfanar da ita ne bisa zarginta da aikata laifuka biyu.
Na farko shi ne ta lalata kayan aiki sannan kuma ta tayar da zaune tsaye a anguwar. Sai dai ba ta amsa duk laifukan ba.
Asali: Legit.ng