Da Ɗumi-Ɗumi: Attajirin Duniya Bill Gates Ya Kamu Da COVID-19

Da Ɗumi-Ɗumi: Attajirin Duniya Bill Gates Ya Kamu Da COVID-19

  • Bill Gates, attajirin dan kasuwa kuma daga cikin wadanda suka kafa kamfanin Micrsoft ya kamu da cutar Korona
  • Gates ya sanar da hakan ne ta shafinsa na Twitter yana mai cewa ciwon bai masa mugun kamu ba saboda ya yi rigakafi
  • Attajirin ya kara da cewa a halin yanzu yana bin shawarwarin ma'aikatan lafiya na killace kansa har zuwa lokacin da zai warke

Bill Gates, attajirin dan kasuwa kuma daya cikin wadanda suka kafa kamfanin Microsoft, ya sanar cewa ya kamu da COVID-19.

Gates ya sanar da hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya kara da cewa yana fama da alamomin cutar amma ba mai tsanani ba.

Da Ɗumi-Ɗumi: Attajirin Duniya Bill Gates Ya Kamu Da COVID-19
Attajirin Duniya Bill Gates Ya Kamu Da Korona. Hoto: he Cable.
Asali: Twitter

"Na kamu da COVID-19. Alamomi kadan sun bayyana a jikina kuma ina bin shawarwarin kwararru ta hanyar kebe kaina har sai na warke," ya rubuta.

Kara karanta wannan

Masu cewa ba ni da isasshen lafiya basu da hankali, mahaukata ne: Tinubu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ciwon bai min mugun kamu ba domin na yi sa'a na y rigakafi - Gates

"Na yi sa'a cewa na yi rigakafi har da na biyun kuma ana min gwaji tare da kulawar kwararrun likitoci.
"Karo na farko cikin shekaru biyu, Gidauniyar Gates za su yi taro, kuma na yi sa'a ina cikin tawagar da za su hadu da kowa in musu godiya bisa ayyukansu.
"Za mu cigaba da aiki tare da abokan hadin gwiwa kuma za mu yi duk mai yiwuwa don ganin ba za mu sake samun annoba ba."

Gates ya dade yana kiraye-kiraye da bada shawarwari kan yadda za a kiyayye afkuwar annoba, musamman ta hanyar yin rigakafi da magunguna ga kasashe marasa karfi.

A sakonsa na karshen shekarar 2021, Gates ya nuna damuwa bisa rashin adalci wurin rabon rigakafi, yana mai cewa bullar sabbin na'uika da kallubale na rigakafin, sun janyo cewa har yanzu ba a kai ga karshen annobar ba.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya da ya buɗe wurin gwajin DNA tare da yin rahusa na kashi 70

A wani labarin daban, wani likita wanda ya bude wurin gwajin kwayoyin halitta na DNA a anguwarsu ya bayyana yadda wasu mutane suke barazanar halaka shi a shafin sa na dandalin sada zumunta sakamakon zargin zai zama kalubale ga aurensu.

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel