Gaskiyan abinda ya faru tsakanin Malam Musa Lukuwa da yan kwamitin ganin wata, Simwal Jibrin

Gaskiyan abinda ya faru tsakanin Malam Musa Lukuwa da yan kwamitin ganin wata, Simwal Jibrin

Daya daga cikin mambobin kwamitin ganin wata ta kasa, Simwal Jibrin, ya yi martani kan faifan bidiyon dake kafafen sada zumunta na jawabin Malam Musa Lukuwa.

Malam Lukuwa, shine limanin da yayi Sallah ranar Lahadi sabanin umurnin Sarkin Musulmi da yace ayi Sallah ranar Litinin.

A dogon jawabin da Simwal ya daura ya shafin kwamitin duban watan na Facebook, ya yi watsi da jawabin da Malam Lukuwa yayi ga abinda ya gudana tsakaninsu.

Simwal Jibrin/Malam Lukuwa
Gaskiyan abinda ya faru tsakanin Malam Musa Lukuwa da yan kwamitin ganin wata, Simwal Jibrin Hoto: Simwal Usman Jibrin/Sheikh Musa Ayuba Lukuwa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga jawabinsa:

" Akwai wani faifan bidiyo da ake yadawa na Malam Musa Lukuwa a Sokoto, wanda ya yi ikirarin ganin jinjirin watan Shawwal 1443H a ranar 29 ga Ramadan 1443H/30 ga Afrilu 2022G.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

A faifan bidiyon ya yi ikirarin cewa mambobin kwamitin kula da wata na kasa sun ziyarce shi inda suka bukaci ya gabatar da lacca kan ganin wata a masallacinsa a shekarar 2018, inda ya kara da cewa ya hana tawagar izinin ba da laccar, maimakon haka, ya ce kawai zai bari ayi muqabala ne a masallacinsa akan ganin wata. Ya kara da cewa a cikin faifan bidiyon, cewa mambobin kwamitin sun amince su dawo ayi muqabala a washegari amma ba su dawo ba.

Gaskiyar lamarin da kuma abin da ya faru a zahiri shi ne kamar haka:

Mambobi biyu na kwamitin ganin wata na kasa Malam Salihu Muhammad Yakub da Malam Ja’afar Abubakar sun je Sokoto domin sanya ido kan ganin jinjirin watan Shawwal 1439H a karshen watan Ramadan 1439/2018.

‘Yan kungiyar sun yanke shawarar kai wa Malam Musa Lukuwa ziyarar tattaunawa ne saboda a hukumance mun cika kwanaki 30 a watan Ramadan 2018 amma Malam Musa ya yi ikirarin cewa mutanensa sun ga jinjirin watan Ramadan ne a ranar 29 ga watan Ramadan

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Mallam Musa ya zo da sharudda guda uku:

1) Mambobin kwamitin ganin wata na kasa su dawo ranar 29 ga watan Shawwal (Kwanan watan shi, alhalin ranar 28 ga watan Shawwal ne a Najeriya).

2) Wurin neman jinjirin watan zai kasance a wurin da Malam Musa da tawagarsa suka amince da shi.

3) Idan aka ga jinjirin watan a ranar 29 ga watan Shawwal bisa ga ranar Mallam Musa (wato 28 ga watan Shawwal ne wanda Mai alfarma Sarkin Musulmi ya ayyana), kwamitin kula da ganin wata na kasa zai buga takardar neman yafiya ga jama'a tare da daidaita ranar zuwa ga kwanan watan shi.

‘Yan kwamitin ganin wata na kasa sun amince da sharuddan amma Mal Ja’afar Abubakar (mamba na kwamitin kula da wata na kasa) ya kara da cewa:

Idan ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a ranar 29 ga watan Shawwal (Kwanan watan Mal Musa), kuma aka gan shi washegari wato 29 ga watan Shawwal, shi ma Mal Musa ya fitar da takardar neman yafiya ga jama'a kuma ya daidaita lissafinsa zuwa lissafin mai Alfarma Sarkin Musulmi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

A ranar 29 ga watan Shawwal na Mallam Musa (28 ga watan Shawwal a hukumance), Wakilan kwamitin ganin wata na kasa Simwal Jibril, Mal Salihu Muhammad Yakub, Mal Ja'afar Abubakar, da Mal Usman Mahmud suka tashi zuwa wurin da aka amince da su, wani tudu dake hanyan Sokoto - Wamako tare da tawagar Mallam Musa Lukuwa, karkashin jagorancin wani Mallam Aminu Shugaba da wasu mutane uku. Yanayin sama na da kyau sosai babu gajimare, kura , ko hadari, mun nemi jinjirin watan amma ba mu iya gani ba. Mun sake haduwa a wurin washegari 30 ga Shawwal na Malam Musa Lukuwa (29 ga Shawwal a hukumance na Mai Alfarma Sarkin Musulmi) yanayin sama na da kyau amma har yanzu ba mu ga jinjirin watan ba, sai muka amince mu sake dawowa rana mai zuwa.

A ranar 30 ga Shawwal na Sultan (31 ga Shawwal na Mallam Musa ), yanayin sama na da kyau Allah Ya sa duka muka ga jinjirin watan.

Kara karanta wannan

Billahil lazi la ilaha illahuwa za mu rike maka amanarka – Gawuna ga Ganduje

Washegari muka je mu gana da Malam Musa Lukuwa a gida domin tattauna sakamakon kokarin da aka yi na ganin jinjirin dare uku amma aka ce mana ba ya gida, ya tafi gona kuma ba zai dawo ba sai bayan sallar isha’i. Washegari tunda mun gama aikin da muka zo yi a Sakkwato na wannan shekarar, muka bar Sakkwato zuwa wurare daban-daban, ba mu sake yin wata magana da Malam Musa ba.

Wannan shi ne ainihin abin da ya faru tsakanin kwamitin ganin wata na kasa tare da Malam Musa Lukuwa. Abin takaici ne duk da haka, har yanzu ya ci gaba da yin watsi da sanarwar hukuma ya kuma cigaba da yada da'awar ganin wata. Allah Ta'ala Ya shiryar da shi da mu zuwa ga gaskiya. Ameen."

Asali: Legit.ng

Online view pixel