Mai daki da Lauyan Kanu sun kai karar Gwamnatin Najeriya har Majalisar dinkin Duniya

Mai daki da Lauyan Kanu sun kai karar Gwamnatin Najeriya har Majalisar dinkin Duniya

  • Lauyan Nnamdi Kanu ya aikawa Jakadan kasar Birtaniya a majalisar dinkin Duniya wani korafi
  • Bruce Fein da Mai dakin shugaban kungiyar IPOB, Uche Kanu ne su ka sa hannu a wannan takarda
  • Ana tuhumar Gwamnatin Najeriya da ta Kenya da saba doka wajen kinkimo Kanu daga Nairobi

United States - Ba’Amurken lauyan da yake kare Nnamdi Kanu, Bruce Fein ya kai korafi game da gwamnatin Najeriya da Kenya a majalisar dinkin Duniya.

The Cable a wani rahoto da ta fitar a ranar Lahai, 10 ga watan Afrilu 2022, ta ce lauyan ya na karar yadda aka kama Nnamdi Kanu, aka dawo da shi Najeriya.

Bruce Fein da mai dakin shugaban kungiyar na IPOB, Uche Kanu su ka sa hannu a wannan korafi da aka aikawa Jakadan Birtaniya a majalisar dinkin Duniya.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke magidanci da bindiga, carbin harsashi 20, shanu 31 da tumaki 28 a Bauchi

Ana sa rai wannan takardar ta je ofishin Barbara Woodward wanda shi ne ke wakiltar gwamnatin Birtaniya a majalisar dinkin Duniya a Amurka.

Uwargidar Nnamadi Kanu da lauyan na sa, sun bukaci majalisar tsaro ta UN ta binciki rawar da kasashen Kenya da Najeriya su ka taka wajen ram da Kanu.

Wadannan mutane su na zargin cewa an saba doka a kokarin kama Kanu, a dawo da shi Najeriya. Tun da ya dawo yake tsare, inda ake ta shari'a da shi a kotu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai dakin Kanu
Matar Mazi Kanu, Uchechi Okwu Kanu Hoto: www.premiumtimesng.com

A hukunta wanda ya saba doka

Uche da Fein sun bukaci a kafa kotu na musamman da zai yi wannan bincike, tare da hukunta duk wadanda aka samu da laifi tsakanin kasashen Afrikan biyu.

Sahara Reporters ta ce masu korafin sun dogara ne da sashe na bakwai na dokar majalisar dinkin Duniya wajen kai karar dukunkuno Kanu da aka yi daga ketare.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi

A watan Yunin 2021 ne gwamnatin tarayya ta hada-kai da kasar Kenya, aka cafko Kanu a birnin Nairobi, aka kunshe shi zuwa Najeriya ba tare da amincewarsa ba.

Da hannun Buhari da Kenyatta - Fein

Korafin ya ce ana zargin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, Ministan shari’a, Abubakar Malami da shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta da aikata laifi.

Don haka lauya da matar shugaban haramtacciyar kungiyar su ka ce shugabannin kasashen ba za su iya binciken laifin da su na da hannu dumu-dumu a ciki ba.

Irin wannan kwamiti ne majalisar dinkin Duniya ta kafa a wani zama wanda ya yi bincike wajen gano wadanda suke da hannu wajen kashe Rafik Harari a Lebanon.

Najeriya ta na tafka asara

A makon jiya ne aka ji cewa Shugaban kamfanin man NNPC, Mele Kolo Kyari ya bayyana a gaban majalisar wakilan tarayya, ya bayyana irin ta'adin da wasu ke yi.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau

Mele Kyari ya yi tir da aikin masu fasa bututun danyen mai da masu matatan da ba su da rajista. Wannan danyen aikin ya jawo ana asarar N1.5bn duk a shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel