Rashin Tsaro: Birtaniya Ta Gargaɗi Ƴan Kasarta Game Da Ziyartar Jihohin Arewa 7 a Najeriya
- Kasar Birtaniya ta fitar da takardar bada shawarwari ga yan kasarta masu sha'awan zuwa Najeriya bayan hare-haren baya a arewa
- Gwamnatin na Birtaniya ta lissafa a kalla jihohi 7 na arewacin Najeriya da ta gargadi mutanenta su kauracewa
- Kasar ta Ketare ta shawarci yan kasarta da yanzu suke Najeriya su rika takatsantsan su kuma rika sa ido kan abubuwan da ke faruwa a kullum
Kasar Birtaniya da aka fi sani da UK ta fitar da shawarwari ga yan kasarta masu sha'awar kawo ziyara Najeriya. Ta lissafa jihohi 12 a Najeriya da ta ce a kauracewa.
Takardan shawarwarin da UK ta fitar da ofishin harkokin kasashen waje da hadin kan kasashen da Birtaniya ta raina, FCO, ya zo ne bayan hare-haren da yan bindiga suka kai a arewa a baya-bayan nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na Intanet, da aka yi wa kwaskwarima a ranar 29 ga watan Maris na 2021 kuma yana nan har yanzu a ranar 30 ga watan Maris, ta nuna damuwarta kan harin da aka kai filin jirgin sama inda aka kashe a akalla mutum daya.
Gwamnatin na kasar wajen ta shawarci yan kasarta da ke Najeriya su rika sauraron labarai, su kuma guje wurin taron dandazon mutane.
Ofishin na FCO ta gargadi yan kasarta game da kai ziyara jihohi kamar haka:
1. Borno state
2. Yobe state
3. Adamawa state
4. Gombe state
5. Kaduna state
6. Katsina state
7. Zamfara state
Sai jihohin yankunan da akwai teku kamar Delta, Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da Cross Rivers.
FCO ta shawarci a guji tafiye-tafiye amma idan ya zama dole ana iya zuwa jihohin:
1. Bauchi state
2. Kano state
3. Jigawa state
4. Niger state
5. Sokoto state
6. Kogi state
7. Abia state
Sai kuma kilomita 20 daga iyakokin Jihar Niger da Kebbi.
Da yankunan da babu teku a Jihohin Delta, Bayelsa da Rivers.
Ta kuma ja kunnen yan kasarta su kasance masu saka ido da lura a koda yaushe, su kuma sanar da wasu inda za su tafi.
Asali: Legit.ng