Daga karshe: Saudiyya ta dage wasu dokokin Korona yayin da Ramadana ke karatowa
- Kasar Saudiyya ta bayyana dage wasu daga cikin dokoki da ka'idojin cutar Korona da ta addabi duniya
- Wannan na zuwa ne makwanni kadan gabanin Azumin watan Radamana, inda ake sa ran zuwan masu Umrah
- Korona dai ta jawo dakatarwa da rage adadin mahajjata a shekarun 2022 da 2021, lamarin da ya ja hankalin duniya
Saudiyya - Kasar Saudiyya ta ce ta dauke mafi yawan takunkumin Korona da suka hada da ba da tazara yayin sallah da kebe masu shigowan da suka yi rigakafin Korona, matakan da za su iya saukakawa masu shiga kasar domin ibada.
Shawarar ta ce hakan zai shafi wurare daban-daban na taro a kasar, ciki har da masallatai, in ji majiyar ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.
Sai dai, za a bukaci mutane suke sanya takunkumin fuska a wuraren da suke rufe, bisa ga shawarar, wacce ta fara aiki ranar Asabar.
Kasashen da a baya Saudiyya ta sanya wa takunkumin shiga kai tsaye sun hada da Afirka ta Kudu, Namibia, Botswana, Zimbabwe, Lesotho, Eswatini, Mozambique, Malawi, Mauritius, Zambia. Madagascar, Angola, Seychelles, Comoros, Najeriya, Habasha, da Afghanistan, rahoton Khaleej Times.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Cutar Korona ta kawo cikas ga aikin hajji ga musulmi, wadanda galibi su ne manyan hanyoyin samun kudaden shiga ga masarautar Saudiyya, inda suke samun kusan dala biliyan 12 a duk shekara.
Bayar da ziyarar aikin hajji wani lamari ne da ke da martaba ga mahukuntan Saudiyya, wadanda kula da wurare masu tsarki na Musulunci shi ne mafi karfin tushensu na halaccin siyasa.
A 2021, barkewar cutar Korona ta tilastawa hukumomin Saudiyya rage adadin mahajjata na shekara ta biyu tun bullar cutar, inda mutane 60,000 ne kawai da suka yi allurar riga-kafi da mazauna masarautar suka yi hajji.
Tun bayan barkewar cutar, Saudiyya ta samu sama da mutane 746,000 da suka kamu cutar Korona, 9,000 daga cikinsu sun mutu, a cikin mutane kusan miliyan 34 da ke kasar.
Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro
A wani bangare na kokarin ganin an kiyaye dokar lafiya, hukumar babban birnin tarayya Abuja ta sanar da haramtawa wuraren shakatawa da bukukuwa da majami’u na addini da ke da mabiya sama da 50 yin taro.
Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 25 ga Disamba, ta ce an sanar da matakin ne sakamakon sake barkewar Korona.
Hakazalika, gwamnati ta ce gazawar mazauna Abuja wajen daukar matakan kariya masu sauki abin damuwa ne ga lafiyar al'umma.
Asali: Legit.ng