Manyan 'yan crypto na magana: Kasuwa ta kara yin muni, an sake tafka mummunan asara

Manyan 'yan crypto na magana: Kasuwa ta kara yin muni, an sake tafka mummunan asara

  • Premium cryptocurrency, Bitcoin da sauran manyan tsabobin kudaden intanet sun zube a ranar Litinin, Janairu, 24, 2022.
  • Sama da Naira Tiriliyan 53 aka yi asara a kasuwar crypto yayin da ake ci gaba da faduwa cikin mako biyar na asarar 'yan crypto
  • Masu sharhi sun yi imanin cewa Bitcoin na iya kara faduwa zuwa Naira miliyan 12 yayin da ake janye kudaden na intanet tare da hannayen jari a duniya

Bitcoin da sauran manyan kudaden intanet sun yi faduwar kusan Naira tiriliyan 54 a cikin sa'o'i 24 yayin da suke ci gaba da faduwar kasa, faduwar da ta fara sama da makonni biyar a jere kenan.

Bitcoin ya ragu da kusan 4% cikin 100% akan Naira miliyan 14, in ji Coin Metrics da Ether mai faduwar kusan 7% bisa 100% zuwa Naira miliyan biyu.

Kara karanta wannan

Jihar Kebbi: Yadda 'yan bindaga suka hallaka da dama, tare da sace wasu saboda kin biyan haraji

Manyan 'yan crypto na magana: Kasuwa ta kara yin muni, an sake tafka mummunan asara
Manyan 'yan crypto na magana: Kasuwa ta kara yin muni, an sake tafka mummunan asara | Hoto: Flashpop
Asali: Getty Images

A ranar Litinin, 24 ga Janairu, 2022, dukansu sun yi kasa a matsayi mafi karanci tun watan Yulin bara. Haka kuma sun fadi da 50% cikin 100% na kololuwar darajarsu a tarihin crypto, a cewar wani rahoton CNBC.

Faduwa kudaden ke yi tare da hannun jari na duniya

Kudaden crypto suna faduwa tare da hannayen jari na duniya wadanda suka rugujewa tun farkon wannan shekarar.

'Yan crypto da dama suna ta sayar da kadarorinsu kamar hannun jari a fannin fasaha yayin da ake shirin kawo tsauraran manufofin kudi daga Babban Bankin Tarayyar Amurka.

Bisa ga binciken CNBC, 'yan crypto suna sake nazarin karin sarrafa lamurra a kasuwar crypto.

A makon da ya gabata, babban bankin kasar Rasha ya bi sahun babban bankin Najeriya tare da bayyana yiyuwar haramta kasuwanci da hakar tsabobin crypto.

Kara karanta wannan

'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa

Yiyuwar rushewar farashin Bitcoin

Saboda yanayin kasuwa na yanzu, Bitcoin ta yiwuwa ya gangaro zuwa Naira miliyan 12.4 zuwa Naira miliyan 13.2, in ji Vijay Ayyar, Mataimakin Shugaban kamfanin hada-hadar crypto na Luno a duniya.

Ayyar ya ce idan Bitcoin ya tsaya a kusan $30,000 na kusan mako daya, za a iya samun wani tushen nazari a wadannan matakan sabbin ka'idoji kafin kasuwar crypto ta motsa.

A tun farko, masu zuba kudadensu a duniyar crypto sun fuskanci babbar asara a sashen Bitcoin da wasu tsabobin crypto suka rage darajar ta shafe sama da N296.68bn na kadarori a cikin kasa da sa'o'i 24.

Bayanai daga CoinDesk sun nuna cewa Bitcoin ya fadi da kasa da 8% kuma koma kan farashin $38,5K a farkon sa'o'in ranar Juma'a.

Faduwar darajar Bitcoin ta kai ga durkusar da lalitun 'yan crypto sama da 185,480 inda akalla suke bukatar neman sabon jari don ci gaba da harkalla.

Kara karanta wannan

'Yan crypto sun shiga tasku: Miliniyoyi a duniyar crypto sun karye, harka ta kara lalacewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.