Korona: Saudiyya ta yi ƙarin haske game da batun ɗage Umrah a bana

Korona: Saudiyya ta yi ƙarin haske game da batun ɗage Umrah a bana

  • Mahukunta a kasar Saudiyya sun bayyana cewa babu shirin dage aikin Umrah saboda cutar korona
  • Sai dai shugaban masallatai masu tsarki na Saudiyya ya sanar da dawo da dokar bata tazara da saka takunkumin fuska
  • Hakan na zuwa ne sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar ta korona a baya-bayan nan amma kasar ta ce ta dauki matakai na tsare mutane

Gwamnatin kasar Saudiyya ta yi watsi da jita-jitar dangane da batun dage yin aikin Umrah na bana saboda karuwar cutar COVID-19 wacce aka fi sani da korona, Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya daga Ma'aikatar Aikin Hajji da Umrah ta shaidawa Haramain Sharifain cewa ba ta da shirin dage Umrah.

Korona: Saudiyya ta yi ƙarin haske game da batun ɗage Umrah a bana
Korona: Ba mu da shirin dage aikin Umrah na bana, Saudiya. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Filato: Kada wata kungiya ta dauki doka a hannunta, in ji Buhari

Ta yi kira ga masu niyyar kai ziyara da masu zuwa aikin Umrah da su bi dokoki da ka'idoji da hukumomin kasar suka gindaya domin tsare lafiyar su.

Shugaban hukumar da ke kula da masallatai biyu masu tsarki, a baya-bayan nan ya sake dawo da dokar bada tazara tsakanin mutane a masallatan biyu bayan samun karuwar cutar ta COVID-19, Daily Trust ta ruwaito.

Babban limamin masallacin Sheikh Yasir Al Dossaary ya sanar da hakan kafin sallar azahar a ranar Alhamis, yana mai cewa:

"Muna kira ga dukkan masu aikin Umrah da masu ziyara su kiyaye dokar bada tazara tare da saka takunkumin fuska a ko yaushe domin tsare kansu da sauran mutane."

Mutane biyu sun rasu sakamakon cutar COVID-19

Kasar ta Saudiyya ta sanar da cewa mutane biyu sun mutu sakamakon cutar da COVID-19 sannan sabbin mutum 5,499 sun kamu a ranar Alhamis.

A cikin sabbin wadanda suka kamu, 1565 a Riyadh ne, 877 a Jeddah, 474 a Makkah, 239 a Madinah, 198 a Dammam, 137 a Taif, 110 a Qatif, 103 aAl-Khobar, 102 a Hofuf, da 100 a Khulais.

Kara karanta wannan

FG ta bayyana sharudda 5 da ta gindaya wa Twitter kafin dage dokar haramci

An kuma samu kasa da 100 a wasu biranen.

Jimillar wadanda suka kamu a kasar ta Saudiyya sun kai 555,035 bayan 2,978 sun warke daga cutar.

Mutum 8,901 ne suka mutu sakamamakon cutar a kasar. An kuma yi wa mutane fiye miliyan 53.3 rigakafi kawo yanzu.

Attajirin Yariman Saudiyya zai siya ƙungiyar ƙwallon ƙafa a Faransa

A wani labarin daban, Yariman Saudiyya masoyin 'kwallon kafa da kudi', Yarima Abdullah bin Mosaad yana dab da mallakar kungiyar kasar Faransa ta Chateauroux, The Punch ta ruwaito.

Yariman wanda ya mallaki kungiyoyin Sheffield United, Beerschot a Belgium, Kerala United a Indiya da Al Hilal United a UAE yana daf da kara sabuwar kungiya kan wadanda ya ke da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164