Allahu Akbar: Ana gobe Kirsimeti, an mayar da wata gagarumar coci zuwa Masallaci a Turkiyya
- Ana gobe ranar Kirsimeti, an mayar da wata katafariyar coci zuwa Masallaci a yankin Adrianopilis/Edirne a garin Ainos/Enez da ke kasar Turkiyya
- Ali Erbas, shugaban al'amuran addinin Islama na Turkiyya ya bayyana hakan a wallafar da yayi a shafinsa na Twitter
- Ya sanar da tsananin farin cikin da suke ciki bayan da aka kaddamar da Masallacin inda yayi addu'ar Allah ya cigaba da daukaka Musulunci
Turkiyya - Wannan al'amarin ya auku ne a Adrianopilis/Edirne a garin Ainos/Enez inda aka mayar da wata katafariyar coci masallaci.
Kamar yadda malaman fannin kashe-kashen Girka suka shaida, kashe-kashen ya fara aukuwa ne a 1913, kafin yakin duniya na daya, Edirne a gabashin Thrace take.
Bayan dawo da cocin bisa umarnin GDI, Cocin Hagia Sophia da ke Ainos (Enez), a Adrianoupolis (Edirne), ta koma masallaci ranar jajibarin Kirsimeti.
Masallacin Muhammed mai nasara ya koma masallacin nasara a shekarar 1456 sannan an kara bude shi a matsayin masallacin Muhammed mai Nasara.
Sakamakon girgizar kasar da aka yi a yankin ya sa ba a sake bude cocin ba. Ali Erbas ya kara bude masallacin bayan shekaru 56 don a yi sallar Juma’a.
Rahoton The Echedoros-a.gr ya bayyana yadda Erbas ta dauki Musulunci a matsayin al’ada wacce su ka dauka matukar muhimmanci akan masallaci.
An yi addu’o’i da kuma jawabi bayan yanke kyallen kaddamar da masallacin.
“Bayan an kaddamar da masallacin Hegia Sophia a Istanbul shekarar da ta gabata, ga shi yau mun kara haduwa don kaddamar da masallacin Hegia Sophia a Ainu-Edirne,” kamar yadda shugaban harkokin addini, Ali Erbas ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ya kara da cewa:
“Mun kai ziyara Balkans a watannin da suka gabata. Da zarar mun kalli ginin masallacin zuciyarmu tana mana dadi. Ana aiwatar da ibada a masallacin Hagia Sophia a Edirne. Muna fatan Ubangiji ya albarkaci masallacin. Wannan yana nuna hadin kai da soyayya kamar yadda muke a dunkule anan.”
A karon farko, an yi bikin gagarumin bikin Kirsimeti a kasar Saudi Arabiya a 2021
A wani labari na daban, a karon farko, an yi shagulgula na gani da fadi don bikin kirsimeti a kasar Saudiyya. A shekarar 2021 ne mutanen kasar Saudi Arabiya suka sha bukukuwa saboda kirsimeti. Da alamu wannan shekarar an yi shagulgula iri-iri tun bayan dage dokokin kare kai daga cutar korona.
Babu shakka kirsimeti biki ne wanda kiristoci su ke dabbakawa a kowacce karshen shekara kuma ya na kasancewa lokacin rani, Saudi Gazette ta ruwaito.
Kiristoci da dama da ke kasar Saudiyya sun nuna jin dadinsu akan damar da suka samu a karo na farko suka yi shagulgulan kirsimeti a shekarar nan. Duk da dai a shekarun baya su na shagulgulan amma bai bayyana karara ba har ya zama gagarumi kamar na wannan shekarar.
Asali: Legit.ng